Rahotanni sun yi nuni da cewa, harin ya auku ne ranar 25 ga Nuwamba da daddare, kuma mutane huɗu sun jikkata, inda yanzu haka suke karɓar magani a asibiti.

An kashe aƙalla mutum 16 a wani harin 'yanbindiga a Jihar Filato ta Nijeriya- Rahotanni

Aƙalla mutane 16, ciki har da yara da tsofaffi, aka kashe yayin wani hari da 'yanbindiga suka kai ranar Laraba da daddare a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Bassa ta Jihar Filato a tsakiyar Nijeriya.

Harin, wanda rahotanni suka ce an kai shi a yankin Tafi Gana, wani ƙauye da ke Kyie Ihwien, kusa da Jebbu Miango, ya kuma jikkata mutane huɗu, waɗanda ke karɓar magani a wasu asibitoci a halin yanzu.

Kazalika a cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Ƙungiyar Cigaban Al'ummar Irigwe (IDA), Sam Jugo ya fitar, ta bayyana cewa maharan na ɗauke da manyan bindigogi da wasu makamai masu haɗari.

A cewar ƙungiyar, lamarin ya jefa mazauna yankin cikin firgici, inda aka gano gawarwakin mutane kusan 16 a wayewar safiyar ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba.

Basaraken yakin, Nggwe Gado Dama, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai rahoton harin ga ofishin 'yansanda na ƙaramar hukumar Bassa da na kwamandan rundunar Operation Enduring Peace ta sashe na uku.

Ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa wurin da harin ya auku a lokacin da aka fitar da wannan sanarwar.

Ƙungiyar Cigaban Al'ummar Irigwe ta yi Allah wadai da kisan, tare da kira ga mazauna yankin da kada su ɗauki doka a hannunsu, inda ta buƙace su da su bai wa jami'an tsaro damar gudanar da bincike da kuma tabbatar da hukunta waɗanda ke da hannu a harin.

Haka kuma, ƙungiyar ta miƙa ta’azziyarta ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Rigwe baki ɗaya bisa wannan babban rashi.

Sai dai ana ta bangaren rundunar 'yansandan jihar Filato ta bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai 17, yayin da wasu huɗu suka jikkata.

A sanarwa da Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yansandan jihar, SP Alfred Alabo ya fitar ranar Alhamis, ta ce bayan samun rahoton harin, rundunar ta gaggauta tura jami'anta zuwa wurin da lamarin ya faru.

Sai dai ya ce da maharan suka hango jami'an 'yansandan suna tunkarar wurin, sai suka tsere zuwa cikin dazukan da ke kewaye da yankin.

‘‘Binciken farko da jami'an bincike suka gudanar ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:55 na daren ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, lokacin da wasu mutane ɗauke da makamai suka kutsa cikin al'ummar tare da buɗe wuta kan mazauna yankin.

Sakamakon haka ne mutane 17 suka rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka samu munanan raunuka daban-daban,’’ in ji shi.

Ya ƙara da cewa ‘‘an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa ta musamman, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiye gawarwaki na asibiti domin ci gaba da bincike.’’

Rundunar 'yan sandan ta kuma ce kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sunday Okoebor, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ta himmatu wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan hari.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: TRT Afrika Hausa

#