Dollar

38,8522

0.25 %

Euro

43,5235

-0.14 %

Gram Gold

4.042,3600

0.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ministan Tsaron India Rajnath Singh ya ce ya kamata a sanya idanu kan ma’ajiyar makaman nukiliyar Pakistan karkashin hukumar kula da sinadarin atom ta MDD, inda Islamabad ta ce ya kamata kasashen duniya su binciki kasuwar bayan fage ta India.

India da Pakistan na zargin juna da rashin iya kula da ma’ajiyar nukiliya

India da Pakistan sun zargi juna a ranar Alhamis da gaza kula yadda ya kamata da cibiyoyin makaman nukiliyarsu, inda suke kira ga duniya da sunya idanu kan ma’ajiyar makaman nukiliya na juna, bayan kasashen sun kaucewa yiwuwar gwabza yaki.

Ministan Tsaron India Rajnath Singh ya ce ya kamata a sanya idanu kan ma’ajiyar makaman nukiliyar Pakistan karkashin hukumar kula da sinadarin atom ta MDD, inda Islamabad ta ce ya kamata kasashen duniya su binciki kasuwar bayan fage ta India.

Rikicin baya-bayan nan tsakanin India da Pakistan ya janyo damuwa a duniya kan tsoron na iya juye wa zuwa babban yaki, an samu cim ma tsagaita wuta a ranar Asabar.

“Na so yin tambaya ga duniya: shin Nukiliya na da tsaro a hannun kasa muguwa da ba ta san me take yi ba?” Singh ya fada wa dakaru a sansanin soji na Srinagar a yankin Kashmir da ke karkashin ikon India.

”Na yi amanna cewa ya zama tilas a sanya idanu kan makaman nukiliyar Pakistan,” in ji Singh.

A wata sanarwa da aka fitar bayan awanni, Ministan Harkokin Wajen Pakistan ya ce kamata ya yi IAEA ta binciki '“Yawan sata da fataucin kayan nukiliya a India.”

“Wadannan abubuwa na nuni ga wanzuwar kasuwar bayan fage da ake amfani da kayan nukiliya a cikin ta a India.”

Tsagaita wuta

A ranar 7 ga Mayu ne rikici ya barke a lokacin da India ta kai hari kan abin da ta kira “sansanin 'ta’addanci” a Pakistan, bayan harin da aka kai a India a watan Afrilu a yankin Kashmir da ke karkashin ikon India tare da kashe mutum 26.

New Delhi ta dora alhakin kai harin kan ‘yan tayar da kayar baya da ke samun goyon bayan Islamabad - hari mafi muni da ya kashe fararen hula a yankin Kashmir na India a cikin shekaru. Pakistan ta musanta zarge-zargen.

Bayan kwanaki hudu na hare-haren jirage marasa matuka ga juna, an yi musayar makamai masu linzami da atilari, inda aka kashe kusan mutane 70 da suka hada da mata da yara kanana daga bangarorin biyu.

Indiya da Pakistan na da makaman nukiliya, kuma mambobin IAEA ne, da ke kula da amfani da makaman nukiliya.

Tun shekarun 1990 India ta habaka makaman nukiliya da makamai masu linzami masu cin gajeren zango. A yanzu ana gwajin masu cin dogon zango, kamar yadda kwararru ke fadi.

Pakistan kuma ta samar da nata makaman nukiliyan masu matsakaici da gajeren zango.

Ministocin Pakistan sun sha nanata cewar zabin nukiliya ba shi ne a kan teburi ba. Sun ce har yanzu ba a aika sammaci ga hukumar gwamnati da ke kula da nukiliyar ba.

Kakakin sojin Pakistan Ahmed Sharif Chaundry ya bayar da rahoto a ranar Lahadi cewa rikicewar rikici tsakanin “masu makamin nukiliya biyu” abu ne “da ba za a karba ba kuma”.

“Wannan rikici na iya janyo mutuwar mutane biliyan 1.6, to a gaskiya, babu sararin yaki tsakanin India da Pakistan,” in ji Chaundry.

A jawabin da ya yi a makon nan, Firaministan India Narendra Modi ya ce “India ba za ta amince da duk wani bata suna game da nukiliya ba.”

Da fari India ta musanta kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Pakistan a yayin yakin na gajeren lokaci.

“Ba mu kai hari tsaunukan Kirana ba,” in ji babban sojan India Air Marshal A.K. Bharti yayin zantawa da manema labarai, yana nufin wani tsauni mai duwatsu, inda rahotannin kafafan yada labarai na Indiya ke cewa a nan ne Pakistan ta ajiye makamanta na nukiliya.”

Kira da a tsagaita

Saboda tsoron rincabewar rikicin, shugabannin duniya sun yi kira ga bangarorin biyu da su tsahirta inda shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana tsagaita wutar ba zata.

Tsagaita wutar ta fara aiki tun karshen makon da ya gabata, bayan ikirarin farko na karya ta daga dukkan bangarorin.

Sai dai kuma, Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, a wayar tarho da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ranar Laraba, ya bayyana “damuwa kan ci gaba da takala da kalaman tsokana daga shugabancin India, wanda barazana ne ga zaman lafiyar yankin,” in ji sanarwar da ofishinsa ta fitar.

Mayaka sun tsaurara kai farmakai kan bangaren India a Kashmir tun 2019, a lokacin da gwamnatin Modi ta ‘yan kishin kasar India suka kwace ‘yancin cin gashin kai da yankin ke da shi tare da kakaba juya yankin kai tsaye daga New Delhi.

‘Yan sandan yankin Kashmir na India sun ce sun kashe wasu mutum uku da suke zargin ‘yan ta’adda ne a ranar Alhamis a garin Tral, a gundumar Pulwama da ke kudancin Srinagar, babban birni a yankin.

Haka zalika ‘yan sanda sun ce wasu ‘yan ta’adda uku da ake zargi sun mutu a musayar wuta da sojoji a ranar Talatar a kudancin wadin Kashmir.

India da Pakistan na ikirarin mallakar yankin Kashmir, wanda tun 1947 suke rikici a kan iyaka bayan samun ‘yancin kansu daga Turawan Birtaniya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#