Dollar

38,8672

0.32 %

Euro

43,5516

0.09 %

Gram Gold

4.030,3800

-0.08 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arziƙi Ta'annati a Nijeriya, EFCC, ta yi nasara a ƙarar da ta kai wasu 'yan China huɗu da ta kama da laifin ayyukan haƙar ma'adanai a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

Kotu a Nijeriya ta samu 'yan China 4 da laifin hakar ma'adanai ba da lasisi ba

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi ta'annati a Nijeriya, EFCC, ta ce ta samu nasarar hukunta wasu ‘yan China da laifin haƙar ma’adanai a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

An yanke wa waɗanda ake zargin su huɗu, Liang Quin Yong, da Wang Huajie, da Zhong Jiajing, da Long Kechong, hukuncin zaman gidan-kaso na shekaru biyar-biyar saboda laifin.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis 15 ga Mayu, ta ce tun a watan Maris ne aka kama su a wani filin haƙar ma’adanai na kamfanin haƙar ma’adanai mai suna “JLM Mining” a jihar Plateau.

Hukumar ta ce kame ya zo ne bayan samun bayanan sirri kan ‘yan Chinan da ake zargi da haramtattun ayyuka a Jos, babbar birnin jihar Plateau.

Sanarwar ta tabbatar da cewa alƙaliyar babbar kotun tarayya da ke Jos babban birnin jihar Plateau, Mai Shari’a Dorcas V. Agishi ta samu ‘yan China huɗu da laifin da ya jiɓinci haramtattun ayyukan neman ma’adanai.

Bayan kotun ta karanta wa mutanen laifukan da ake zarginsu, sun amsa laifin, inda lauyoyin EFCC, M.O. Arumemi da F.A.I Asemebo suka roƙi kotu ta hukunta su daidai da laifinsu.

A ƙarshe, alƙaliyar ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, sannan ta yankewa ‘yan Chinan huɗu hukuncin shekaru biyar kowannensu, da kuma tarar miliyan guda kowannensu.

Haka nan, kotun ta ba da umarnin korar baƙin daga Nijeriya da kuma haramta musu sake shigowa ƙasar. Sannan za a ƙwace dukiyoyin da suka mallaka a bai wa gwamnatin tarayya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#