Sport
Dollar
38,7847
-0.07 %Euro
43,3500
-0.32 %Gram Gold
3.964,4400
-2.2 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Rundunar sojan ƙasar ta ce ta lura da yadda ‘yan ta’addan ke sauya salon hare-harensu, musamman fara amfani da jirage mara matuƙi masu makamai tun watan Nuwamban 2024.
Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da jerin hare-haren da aka kai kan sansanoninta tare da kwantar da hankulan ‘yan ƙasar cewa tana da ƙarfin iya murƙushe ‘yan ta’addan.
Wannan na zuwa ne bayan ‘yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare kan fararen hula da sojoji a ƙasar kwanan nan.
Kwamandan runduna ta musamman, Operation Hadin Kai, da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin, Manjor Janar Abdulsalam Abubakar, ya tabbatar da hare-haren a wani taron manema labarai a birnin Maiduguri ranar Talata.
Ya ce hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai kan garuruwan Dikwa da Gajiram ba su yi nasara ba, yayin da dakarun Nijeriya da ‘yan ta’addan suka fafata a garin Rann, fadar ƙaramar hukumar Kala Balge.
Sababbin dabarun yaƙi da ta’addanci
A lokacin taron manem labaran, kwamandan rundunar ya tabbatar da hare-haren da aka kai kan sansanoni sojin uku tare da mutuwar sojoji huɗu a Rann.
“A cikin wata biyu da suka wuce, mun kasance muna sake dabaru, muna sake tsare-tsare. Babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya ya ziyarci wajen a makonni biyu da suka gabata, kuma an yi wasu sauye-sauye a filin dagan. Ni ma ina ɗaya daga cikin sauye-sauyen, cikin makonni uku da suka wuce na karɓi ragamar jagorantar yaƙin,” in ji shi.
“Ana ƙara yawan kafafe da jami’ai a filin daga. Abin da ‘yan ta’addan suka koma yi shi ne kai hare-hare kan ɗaiɗaikun wurare da ke da rauni suna amfani da shi wajen yaɗa farfaganda wanda shi ya sa muke sake nazari kan yadda muke tura jami’ai. A jiya kawai, an kai hare-hare Rann da Dikwa da kuma Gajiram. Mun murƙushe dukkan waɗannan hare-haren, idan ban da Rann, inda suka yi nasarar kutsewa zuwa wani mataki, lamarin da ya janyo mutuwar jami’ai [soji] huɗu,” in ji kwamandan.
Yayin da yake tabbatar wa mutane jajircewar sojin wajen kawar da ta’addanci a yankin, Janar Abubakar ya bayyana cewa hare-haren baya-bayan nan ba sa nuna cewa Boko Haram za ta koma irin yadda take da ƙarfi a da.
‘Yan ta’adda na amfani da jirage marsa matuƙa
Janar Abubakar ya bayyana taɓarɓarewar lamarin tsaro yankin Sahel a matsayin muhimmin dalilin da ke taimaka wa sabbin hare-haren.
Ya bayyana cewa sace makamai daga barikin sojoji da kuma yaɗuwar makamai a kan iyakokin Nijeriya na ƙara wa ‘yan ta’addan ƙarfi.
Kazalika ya ce rundunar sojin ƙasar ta lura da wani abin damuwa game da yadda ‘yan ta’addan ke sauya salon hare-harensu, musamman fara amfani da jirage mara matuƙi masu makamai tun watan Nuwamban bara.
Kwamandan ya bayyana wahalar iya gano jirage mara matuƙan ta hanyar amfani da fasahar gano tafiyar jirgi da aka saba da ita, inda ya kwatanta lamarin da yadda ake amafani da jirage mara matuƙa a rikicin Isra’ila da kuma rikicin Yukrain.
“A shekaru biyun da suka wuce, mun shirya yin shelar cewa yaƙin ya ƙare, amma taɓarbarewar tsaro a ƙasashen Sahel ta shafe mu,” in ji shi.
Ya jaddada cewa an samu ci-gaba sosai wajen tabbatar da zaman lafiya idan aka kwatanta da shekaru biyar zuwa goma da suka wuce, inda ya yi ishara da komawar kimanin mutum 200,000 zuwa Malam Fatori da Kukawa a matsayin nasarori na baya bayan nan. Ya bayyana cewa sama da ‘yan ta’adda 20 ne aka kashe kuma aka ƙwato makamai cikin makon da ya gabata kawai
Ya ƙara da cewa cikin watanni biyun da suka wuce sojin ƙasar sun fara sake dabaru da kuma sake tsare-tsare domin tinkarar sabuwar bazaranar da ke kunno kai.
Babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya, Lutanan Janar Olufemi Olatunbosun ya ziyarci fagen dagan kwanan nan, lamarin da ya janyo wasu sauye-sauye ciki har da kama aikin kwamandan rundunar da ke yaƙi da ‘yan ta’addan mako ukun da suka wuce. Ana ƙara tura yawan jami’ai da kayayyaki zuwa yankin.
Kwamandan ya ce duk da ƙalubalen da sojojin ke fuskanta, rundunar sojin ƙasar ta shirya domin murƙushe ta’addanci a cikin ƙanƙanin lokaci, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya su ci gaba goya wa sojojin baya.
Comments
No comments Yet
Comment