Sport
Dollar
38,8058
0.04 %Euro
43,1029
0.05 %Gram Gold
4.036,8900
0.04 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Mazauna kauyuka da dama a gundumar Isa da ke kusa da kan iyaka da Nijar sun tsere daga gidajensu a ranar Asabar zuwa Lahadi, sakamakon barazanar hare-haren da wasu gungun 'yan ta'adda suka yi musu, wadanda suka umarce su da su fice bisa umarnin Turji
Fiye da mutum 5,000 daga ƙauyuka fiye da goma sha biyu a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bar gidajensu bayan gawurtaccen ɗan ta’addan nan Bello Turji ya tilasta musu barin gidajensu, kamar yadda wani ɗan majalisa da kuma wasu mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Litinin.
‘Yan bindigan sun kashe aƙalla mutum 12 inda suka tilasta wa mazauna yankin hijira, kamar yadda Habibu Halilu Modachi, wani ɗan majalisa a yankin ya shaida wa AFP, inda ya ce akwai yiwuwar adadin waɗanda suka rasu ya ƙaru sakamakon yadda ake samun ƙarin rahotanni.
“Tsakanin Asabar da Lahadi, fiye da mutum 5,000 aka tilasta wa barin gidajensu a Bafarawa da wasu al’ummomi da ke kusa da su, sakamakon barazanar kai hari daga Bello Turji.
“Turji ya aika da mutanensa waɗannan ƙauyuka inda ya buƙace su da su yi hijira zuwa Lahadi da rana ko kuma a kashe su,” kamar yadda Modachi ya bayyana.
Mazauna kauyuka da dama a gundumar Isa da ke kusa da kan iyaka da Nijar sun tsere daga gidajensu a ranar Asabar zuwa Lahadi, sakamakon barazanar hare-haren da wasu gungun 'yan ta'adda suka yi musu, wadanda suka umarce su da su fice bisa umarnin Turji.
Masu gudun hijirar suna samun mafaka a garin Isa da Shinkafi a jihar Zamfara mai makwabtaka, da kuma wuraren 'yan uwa a wasu ƙauyuka masu nisa da ke da kwanciyar hankali.
Arewa maso yammacin Nijeriya da arewa maso tsakiya sun sha fama da hare-haren 'yan ta'adda da ake kira 'yan bindiga, waɗanda ke kai farmaki kan ƙauyuka tare da yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
“Ko da safiyar yau, 'yan bindigar sun kashe mutane biyu, sun ji wa tara rauni, kuma sun yi garkuwa da wasu bakwai,” in ji Modachi.
Ahmad Abdullahi, wanda shi ma ya tsere zuwa Isa, ya ce 'yan bindigar sun shiga ƙauyensu suka umarci kowa da ya bar wurin.
“Suna ta harbi ba ƙaƙƙautawa, suna kwashe kuɗi, kayan abinci da duk wani abu mai daraja daga hannun mazauna,” in ji Abdullahi.
Turji, mai shekaru 31, ya bar kiwo ya koma satar shanu da yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa a shekarar 2011.
Ya tsere daga garinsa na Shinkafi a jihar Zamfara zuwa jihar Sokoto inda ya kafa sansanoni bayan hare-haren sojojin Nijeriya ta sama a watan Disamba na shekarar 2021.
Turji ya yi yarjejeniyar zaman lafiya da hukumomin jihar Zamfara sau da yawa, amma daga baya ya karya yarjejeniyar ya ci gaba da kai hare-hare kan al'umma.
Comments
No comments Yet
Comment