Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta halaka 'yan ta'adda da dama a Igze da Malam Fatori da ke Borno a ranar Laraba, sai dai wasu rahotanni na cewa 'yan ta'addan sun kashe wasu daga cikin sojojin, daga ciki har da wani mai muƙamin kyaftin.

Sojojin Nijeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram/ISWAP da dama a Borno

 Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da dama a Jihar Borno.

Sojojin sun halaka ‘yan ta’addan ne a Igze da Malam Fatori da ke Borno a ranar Laraba, 7 ga Mayun 2025.

Sai dai wasu jaridun Nijeriya sun ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kashe wasu daga cikin sojojin, daga ciki har da wani mai muƙamin kyaftin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mayaƙan na Boko Haram suka dawo da kai hare-hare a arewa maso gabas musamman Jihar ta Borno.

Haka kuma harin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban sojin ƙasa na Nijeriya Janar OO Oluyede ya je arewa maso gabas ɗin domin sa ido kan ayyukan dakarun sojin ƙasar.

Boko Haram, wadda ke kai hare-hare a Nijeriya tun daga shekarar 2009, ta yi sanadin mutuwar dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu.

Haka kuma tun daga shekarar 2015, ƙungiyar ta ƙara faɗaɗa hare-haren da take kaiwa zuwa Kamaru da Chadi da Nijar.

Haka kuma an ƙara samun wasu ƙarin ƙungiyoyin ta’addanci da suka ƙara bazuwa a yankin na Sahel inda suka shafi ƙasashe irin su Burkina Faso da Mali duka waɗanda ke maƙwabtaka da Nijar.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#