Sport
Dollar
38,7786
0.39 %Euro
43,8944
0.27 %Gram Gold
4.147,5900
1.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wurin haƙar man Usan, wanda aka gano a shekarar 2002 kuma aka ba da damar [haƙa] a shekarar 2008, ya fara aiki ne a cikin shekarar 2012 kuma a halin ya ƙunshi kimanin rijiyoyin mai nau’i-nau’i 34 da ke a haɗe da bututun mai na ƙarƙashin teku takwas.
Babban kamfanin samar da makamashi ExxonMobil ya shirya domin zuba jarin dala biliyan 1.5 cikin ayyuakansa na cikin teku a Nijeriya, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan harkar mai a ƙasar ta bayyana ranar Laraba.
Shirin zuba jarin, da za a yi tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar 2025 da shekarar 2027, zai mayar da hankali ne wajen farfaɗo da haƙar mai a wurin haƙan man Usan da ke cikin teku, da ke kusa da ɓangare na 139 na haƙar mai a gabashin Neja Delta, kimanin kilomita 70 (mil 43.5) daga gaɓar teku.
Wurin haƙar man Usan, wanda aka gano a shekarar 2002 kuma aka ba da damar [haƙa] a shekarar 2008, ya fara aiki ne a cikin shekarar 2012 kuma a halin ya ƙunshi kimanin rijiyoyin mai nau’i-nau’i 34 da ke a haɗe da bututun mai na ƙarƙashin teku takwas.
ExxonMobil na hangen cim ma hukunci ƙarasa yanke hukunci game da zuba jari a aikin na Usan a ƙarshen shekarar 2025.
Wannan matakin ya dogara ga amincewa da shirinsa na farfado da wurin da kuma samun jari hannayen jari daga abokan huldarsa na cikin gida.
A wata zama ranar Talata tare da Gbenga Komolafe, shugaban hukumar da ke kula da haƙo mai ta Nijeriya (NUPRC), Shugaban kamfanin ExxonMobil a Nijeriya, Shane Harris, ya bayyana cewa wannan alƙawarin zuba jarin dala biliyan $1.5 daban yake da jarin da za a zuba wajen farfado da ƙadarorin cikin teku, ciki har da wuraren haƙar man Owowo da kuma Erha.
Komolafe ya yi maraba da da wannan muhimmin zuba jarin, yana mai cewa wannan ya yi daidai da burin hukumar NUPRC na haɓaka adadin gangar ɗanyen man da Nijeriya ke samarwa zuwa ganga miliyan 2.4 a yini zuwa shekara mai zuwa a ƙarƙashin shirinsa mai taken “Shirin gangar [mai] miliyan ɗaya".
Comments
No comments Yet
Comment