Dollar

38,6058

0.09 %

Euro

43,9796

0.63 %

Gram Gold

4.245,7600

2.7 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

“Na saurari muryar da aka turo aka ce daga Alhaji Garba Dangida ne da kuma Janar Tsiga kuma na yi godiya sosai da wannan voice da na ji, kuma ina fatan Allah ya saka musu da alheri.

Ba mu muka yi allon maraba da Tinubu na Katsina babu ƙorafi ba - Gwamna Radda

Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya Dikko Umaru Radda ya ce ba su ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar.

A wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar don yin martani a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure a Nijeriya kan wani allon saƙo da aka kakkafa a Katsina lokacin da Shugaba Tinubu ya halarci auren ‘yar gwamnan, Gwamna Radda ya ce yana da kyau a dinga bincike kafin yanke hukunci kan abubuwa.

“Na saurari muryar da aka turo aka ce daga Alhaji Garba Dangida ne da kuma Janar Tsiga kuma na yi godiya sosai da wannan voice da na ji, kuma ina fatan Allah ya saka musu da alheri.

“Amma abin da nake so na ce shi ne ya kamata a dinga bincike idan an ji labari a soshiyal midiya ko a zahiri kuma a dinga tambaya,” in ji gwamnan.

Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara da ce-ce-ku-ce daga ko ina a fadin Nijeriya inda masu sharhi ke cewa jihar da ke fama da ƙalubalen tsaro bai kamata ta nuna wa Shugaban Ƙasa cewa ba ta da wani ƙorafi ba.

Sai dai Gwamna Radda ya ce sun tattauna matsaloli uku da ke damun jihar Katsina da Shugaban Ƙasar da suka haɗa da matsalar rashin tsaro da aikin windmill na Rimi da ayyukan filinjiragen sama da aka tsaida.

“Maganar hanyoyi kuwa da kansa (Shugaban Ƙasa) dama ya yi kuma hanyoyin an ba da aikinsu kuma mun shaida wa Shugaban Ƙasa wannan.

Amma a kan batun allon talla da aka rubuta Katsina babu ƙorafi gwamnan ya ce”Maganar billboard da wani ya buga na cewa ‘Katsina ba ƙorafi’ ni a matsayina na gwamna ban ma san an buga shi ba sai da na gani a soshiyal midiya nake tunanin yaya aka buga shi, wa ya buga shi.”

Radda ya koka cewa kuskure ne idan aka dinga jam’i ana zargin mutane a kan abin da a zahirance sun tabbatar ba su yi ba.

“Amma ku manyanmu ne iyayenmu ne idan kun ga wani abu na kuskure kuna iya mana magana muna iya gyarawa, mu kuma mutane ne muma kamar kowa muna iya yin kuskure muna iya yin ba daidai ba.

“Amma dai don Allah a matsayin manya da iyaye idan kun ji abu a soshiyal midiya ku dinga kiranmu ku ji yaya abin ya kasance ba wai a tafi soshiyal midiya a dinga irin wadannan maganganun ba. Ina ga ba za su taimake mu ko kawo mana cigaban da muke bukata ba a Katsina,” a cewar gwamnan.

A ƙarshen saƙon muryar na ranar Talata mai tsawon minti 2.48, Radda ya ce “shugabancin nan idan Allah ya ba ka shi kowa na iya kuskure yana iya daidai. Muna fatan Allah ya dora mu bisa daidan. Amma dai a wannan labarin da aka ba da ba haka yake ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#