Dollar

38,6107

0.02 %

Euro

43,8180

0.07 %

Gram Gold

4.134,2100

0 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an gano yaran ‘yan tsakanin shekaru shida zuwa 10 babu rai a cikin wata mota da aka ajiye a harabar wani gida.

'Yan sandan Nijeriya na bincike kan mutuwar yara biyar a cikin wata ajiyayyar mota a Jihar Nasarawa

Rundunar ‘yan sanda ta fara gudanar da bincike kan mutuwar yara biyar da aka gano a cikin wata ajiyayyar mota a karamar hukumar Obi a jihar Nasarawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an gano yaran ‘yan tsakanin shekaru shida zuwa 10 babu rai a cikin wata mota da aka ajiye a harabar wani gida.

SP Nansel ya ci gaba da cewa rundunar ta samu rahoton gano gawarwakin daga wani mazaunin unguwar Agyaragu inda lamarin ya faru.

“A ranar 4 ga Mayun 2025, da misalin karfe 5.30 na yamma, wani Ozimna Ogbor, mazaunin unguwar Agyaragu ya kai rahoto hedikwatar ‘yan sanda ta Agyaragu cewa yara biyar - Kamsi Onah (namiji, mai shekaru takwas), Somer Onah (namiji, dan shekara shida), Unice Udouchi (mace, 10), Nnaji Nmasomale (mace ‘yar shekara 10) da kuma Chioma Nnaji (mace mai shekaru takwas)—an gano babu rai a cikin wata mota da ke ajiye a harabar gidan wani mutum mai suna Abu Agyeme mazaunin Agyaragu,” in ji wani bangare na bayanin sanarwar.

A cewar SP Nansel, rundunar ta fara aiki ne nan take bayan umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed. Amma an samu yaran a kulle a cikin motar da ke ajiye ba a amfani da ita.

SP Nansel ya yi nuni da cewa, an bai wa iyayen yaran gawarwakinsu bisa bukatar a binne su, sannan duk jikinsu tabon tsananin zafin da ya ƙoƙƙona musu jiki ne.

“Irin wannan lamari mai taɓa ya taɓa faruwa a cikin watan Agustan 2019, lokacin da yara biyu suka rasa rayukansu a cikin wata ajiyayyar mota a Keffi.” Kwamishinan ya nuna matuƙar baƙin cikinsa game da wannan rashin kuma ya jajanta wa iyalan mamatan.

Ya kara da cewa CP din ya gargadi iyaye da masu gadi, da masu ababen hawa da su yi taka tsantsan tare da tabbatar da cewa yara ba sa samun damar shiga motocin da aka ajiye ko aka yi watsi da su ba tare da kulawa ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#