Dollar

38,5967

0.07 %

Euro

43,8224

0.41 %

Gram Gold

4.086,5800

1.69 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Iƙirarin da Baffa Bichi ya yi cewa gwamnatin Jihar Kano tana bai wa Sanata Rabiu Kwankwaso naira biliyan biyu a duk wata ƙarya ce tsagwaronta, in ji wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fitar.

Baffa Bichi maƙaryaci ne, in ji gwamnan Kano Abba Kabir

Gwamnan Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya ce tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Baffa Bichi maƙaryaci ne da ba shi da “kunya”.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi da maraice.

Sanarwar, wadda ta mayar da martani kan zarge-zargen da Baffa Bichi ya yi cewa gwamnatin Jihar ta Kano tana tafka laifuka na cin hanci da rashawa fiye da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta musanta dukkan zarge-zarge waɗanda ta bayyana a matsayin “abin dariya”.

“Zarge-zarge ƙarya ce tsagwaronta kuma abin dariya, Baffa Bichi babban maƴaryaci ne, kuma dukkan abin da ya faɗa ƙarya ce ziryan,” in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

“Musamman, Gwamna ya yi watsi da zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shugaban Tsarin Kwankwasiyya, yana karɓar naira biliyan biyu duk wata daga gwamnatin Jihar Kano.

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana wannan zargi a matsayin “ƙololuwar ci-da-zuci na siyasa da rashi gaskiya.”

Gwamnan ya ce Baffa Bichi ya kwashe fiye da shekara ɗaya a cikin gwamnatinsa amma bai yi waɗannan zarge-zarge ba sai bayan an sallame shi daga aiki bisa rashin iya aiwatar da ayyukansa, yana mai cewa da a ce da gaske yake da sai ya yi zarge-zargen a lokacin da yake cikin gwamnati.

Ya ce zai ci gaba da gudanar da mulki cikin adalci, yana mai yin kira ga al’ummar Jihar Kano ta yi watsi da irin waɗannan zarge-zarge na ‘yan siyasar da ska rasa tasiri.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#