Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da fasahar tattara bayanan sirri domin magance matsalar garkuwa da mutane da ta'addanci a faɗin Nijeriya.

Za mu ƙwato dazukan Arewacin Nijeriya daga hannun 'yan bindiga - Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙwato dazukan Arewa da ma sauran sassan ƙasar daga hannun masu garkuwa mtane domin karɓar kuɗin fansa da ‘yan ta’adda.

Shugaban ya sha wannan alwashi ne a birnin Katsina ranar Asabar a yayin da yake ziyarar aiki ta kwana biyu a Jihar ta Katsina, kamar yadda mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya bayyana a sanarwar da ya fitar ranar.

Sojojin Nijeriya sun kashe gawurtattun ‘yan fashin daji biyar a Zamfara

"Za mu ƙara mayar da hankali wajen amfani da fasaha domin ƙwato dazukanmu. Tsaro batu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya, ba ƙaramar hukuma ko wani yanki ba. Idan har da gaske muna so a zuba jari a Nijeriya, dole mu kawar da matsalar rashin tsaro,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban na Nijeriya ya ce tun da farko ya gana da dakarun tsaron ƙasar inda ya tabbatar musu cewa “za mu yi dukkan abin da ya kamata domin yaƙi da ta’adda da garkuwa da mutane.”
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar wa mutanen da hare-haren ta’addanci suka shafa cewa zai taimaka musu domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#