Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Rundunar sojin ba ta alaƙanta sabon naɗin da ta yi da ƙarin hare-haren da ake samu a arewa maso gabashin ƙasar ba.
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙin da take yi da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin ƙasar bayan ƙaruwar hare-haren ‘yan Boko Haram a yankin a watanni huɗun da suka gabata.
Hare-haren sun kashe fararen-hula da sojoji da dama.
Rundunar sojin ƙasar ta naɗa Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar a matsayin kwamanda na 15 a yaƙin da take yi da ‘yan Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabashin ƙasar, in ji wata sanarwa da runduna ta musamman da aka yi wa laƙabi da ‘Operation Hadin Kai’ ta fitar.
Sanarwar da muƙaddashin mai magana da yawun rundunar Kaftin Reuben Kovangiya, ya sanya wa hannu ta ce a baya Janar Abubakar ya riƙe muƙamin mataimakin kwamandan kwalejin tsaron Nijeriya da kuma kwamandan wani muhimmin aiki a arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Boko Haram da kishiyarta ISWAP, sun zafafa kai hare-hare a arewa maso gabshin Nijeriya cikin ‘yan makonnin nan.
Waɗannan hare-haren sun ƙara fargabar dawowar hare-haren masu iƙirarin jahadin sosai, inda a halin yanzu salon hare-haren ya ƙunshi amfani da jirgi mara matuƙi ɗauke da makamai da kuma bama-bamai da suke ɗanawa kan muhimman hanyoyi, in ji masana harkokin tsaron.
A ranar Talata, ISWAP ta ɗau alhaƙin kai wani hari a jihar Borno wanda ya kashe aƙalla mutum 26, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar a shafin Telegram.
Masu ta da ƙayar bayan sun shafe shekara 15 suna yaƙar dakarun tsaro a arewa maso gabashin Nijeriya, kuma suna yawan amfani da bama-bamai da suke haɗawa wajen kai hare-hare kan fararen hula da dakarun tsaro.
Rundunar sojin dai ba ta alaƙanta sabon naɗin da ta yi da ƙarin hare-haren da ake samu ba.
"Abin taƙici ne cewa Boko Haram na ƙara yawan hare-hare da garkuwa da mutane a cikin garuruwa da dama, kusan kullum ba tare da cewa an ƙalubalance ta ba, lamarin da ya nuna cewa jihar Borno na rasa iko," kamar yadda gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana wa shugabannin dakarun tsaro cikin wannan watan.
Comments
No comments Yet
Comment