Dollar

38,5696

0.32 %

Euro

43,6402

0.19 %

Gram Gold

4.003,9800

0 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rahotanni sun ce an kama ɗan Birtaniyan ne a Legas a lokacin da yake ƙoƙarin hawa jirgin sama zuwa Birtaniya.

Nijeriya ta kama tsohon sojan Birtaniya kan zargin fataucin makamai

Ana binciken wani tsohon sojan Birtaniya a Nijeriya bayan an kama shi kan zargin fataucin makamai yayin da ake fama da matsalar tsaro a ƙasar ta Yammacin Afirka.

Rahotannin da suka fara fitowa daga kafafen watsa labaran Nijeriya sun nuna cewa mutumin da ake zargin sojin Birtaniya ne.

 Sai dai kuma, ofishin jakadancin Birtaniya a Nijeriya ya musanta rahotannin, yana mai cewa mutumin ba ya cikin sojojin Birtaniya a halin yanzu.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba, ofishin jakadancin ta ce an sallami wanda ake zargin bayan ya riƙe ƙaramin muƙami a rundunar sojin Birtaniya.

 “Mutumin da aka bayyana a rahoton kafafen watsa labaran Nijeriya kwanan nan ba ya aiki a halin yanzu a rundunar sojin Birtaniya," in ji wani mai magana da yawun ofishin jakadancin Birtaniya.

Kamu a filin jirgin sama

Ofishin ya ce ba zai ƙara bayani game da mutumin da ke zargin ba, yana mai kafa hujja da dokar kare bayanai ta Birtaniya.

Rahotanni dai sun ce jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin ne a babban birnin kasuwancin Nijeriya, Legas, yayin da yake ƙoƙarin hawa jirgi zuwa Birtaniya.

Kafafen watsa labaran ƙasar sun bayyana a makon da ya gabata cewa wanda ake zargin ɗan ƙasar Birtaniya ne ɗan asalin Nijeriya kuma kamunsa yana da alaƙa da zargin sayen makamai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Neja Delta mai arzikin mai.

 Yankin Neja Delta ya shafe shekaru yana fama da rashin tsaro inda aka riƙa arangama tsakanin dakarun gwamnati da ƙungiyoyin ‘yan bindiga masu fafatukar neman ƙarin kaso a arzikin mai, amma suna yawan garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da kuma lalata bututun mai, lamarin da ke sa tattalin arzikin Nijeriya ke rasa biliyoyin daloli.

Kira domin bincike mai zurfi

Kazalika ƙasar ta Yammacin Afirka tana fama da hare-haren ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ciki har da Boko Haram da ISWAP, tare da masu garkuwa da mutane a arewacin ƙasar.

Masu sharhi sun daɗe suna saka ayar tambaya kan tushen kuɗi da makamai na ƙungiyoyin inda wasu ke nuna cewa suna samun tallafi ne daga waje.

Bayan dawowar Donald Trump kan karagar mulkin Amurka, wani ɗan majalisar dokokin ƙasar ya yi zargin cewa hukumar ba da agaji ta ƙetare ta Amurka, USAID, ta taimaka wajen ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ciki har da Boko Haram.

Masu fafatuka sun yi jerin gwano zuwa ofishin jakadancin Birtaniya a farkon wannan makon domin su yi kira ga gwamnatin Birtaniya ta bai wa hukumomin Nijeriya haɗin kai wajen bincika lamarin na baya bayan nan da ke da alaƙa da ɗan Birtaniya.

Kawo yanzu dai hukumomin Nijeriya ba su ba da cikakken bayani ba.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#