Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sakamakon ya bai wa Nijeriya maki uku muhimmai a rukunin da ke da ƙasashen Morocco da Kenya.

Kofin Afirka na U20: Auwal Ibrahim ya samar wa Nijeriya nasara kan Tunisia a wasan farko

Najeriya ta fara gasar Kofin Afirka na matasa 'yan ƙasa da shekaru 20 (CAF U20 Africa Cup of Nations) karo na takwas da ƙafar dama.

Tawagar ƙasar ta Flying Eagles ta doke Tunisia da ci 1-0 a wasan farko na rukuni B, wanda aka buga a filin wasa na “30 June Air Defence Stadium” da ke birnin Alkahira a Masar ranar Alhamis.

Matashin ɗan wasa Auwal Ibrahim ne ya zura ƙwallon da ta raba gardama tun gabanin tafiya huytun rabn lokaci a wasan, duk da da ma Nijeriya ce ta mamaye wasan wajen samun damarmaki masu yawa.

A minti na 38 ne ɗan wasan Nijeriya Odinaka Okoro ya bayar da kyakkyawan fasin wanda ya kai ga Auwal Ibrahim, wanda bai yi kuskure ba wajen zura ƙwallo daga kusa, don bai wa Nijeriya nasara.

Sai dai bayan nan, ita ma Tunisia ta yunƙuro da gaggawa inda ta kusa farkewa ta hannun Omar Ben Ali da Anis Doubal. Amma mai tsaron ragar Najeriya da masu tsaron baya sun tsaya tsayin-daka. Mafi kyawun damar Tunisia ta zo a minti na 87.

Ƙarfin tawagogin biyu

Sakamakon wasan ya bai wa Nijeriya maki uku masu muhimmanci a rukunin da yake da manyan ƙasashe kamar Morocco da Kenya.

Ita kuwa Tunisia za ta fuskanci ƙarin matsin-lamba kafin wasansu na gaba. A tarihin baya-bayan nan na gasar, Tawagar Tunisia ta je wasan dab da na ƙarshe a shekarar 2021 da 2023.

Najeriya kuwa ita ce ƙasa mafi nasara a tarihin gasar U-20 AFCON, inda ta taɓa cin kofin sau bakwai.

A yanzu ta tsawaita tarihin buga wasan farko na gasar ba tare da yin rashin nasara ba, zuwa wasa takwas cikin gasanni goma na ƙarshe da ta buga.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#