Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ankara ya yi tur da harin da aka kai wa jirgin na fararen hula wanda haɗakar Freedom Flotilla ke gudanarwa.

Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa jirgin ruwa na Freedom Flotilla

A ranar Juma'a, Türkiye ta yi Allah wadai da wani hari da aka kai kan wani jirgin ruwa na farar hula mallakar Haɗakar Freedom Flotilla, abin da ya ƙara ta’azzara halin da mutanen Gaza ke ciki, inda suke fuskantar yunwa sakamakon shafe makonni biyu da hana shigar da kayan agaji da Isra'ila ta yi wa yankin Falasɗinu.

Ankara ta bayyana cewa wannan hari yana barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tsaron teku a cikin ruwan duniya.

Wani jirgin agaji mai ɗauke da mutane 16 da ke kan hanyarsa zuwa Gaza ya samu matsala bayan wani hari da aka kai masa ta amfani da jirgin sama mara matuƙi a safiyar ranar.

Dakarun Malta sun ceto mutanen da ke cikin jirgin bayan harin. Harin ya haifar da ɗaukewar wutar lantarki a cikin jirgin, wanda hakan ya sanya shi cikin haɗarin nutsewa, in ji wata sanarwa daga ƙungiyar Haɗakar Freedom Flotilla da suka mallaki jirgin, wata ƙungiya ta masu fafutuka da ke neman kawo ƙarshen toshewar da Isra’ila ta yi wa Gaza.

“Zuwa kusan ƙarfe 2:13 na dare, an tabbatar da cewa duk mutanen da ke cikin jirgin suna lafiya, amma duk sun ƙi barin jirgin,” in ji sanarwar, tana mai cewa an shawo kan lamarin zuwa ƙarfe 3:45 na dare.

Jirgin, wanda ake kira Conscience, har yanzu yana cikin ruwan ƙasa da ƙasa kuma hukumomi suna ci gaba da sa ido a kansa, in ji sanarwar.

Duk da cewa babu wanda ya ɗauki alhakin harin, ƙungiyar Freedom Flotilla Coalition ta fitar da wata sanarwa da ke zargin Isra'ila da hannu a lamarin.

“Isra'ila tana so ta ringa kai hari da bamabamai kan jiragen agaji don ci gaba da manufofinta na ƙuntata wa mutanen Falasɗinu ta hanyar yunwa a matsayin dabarun yaƙi,” in ji Dr Shahd Hammouri daga Jami'ar Kent a cikin sanarwar.

Francesca Albanese, jami’a ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan Falasɗinu, ta bayyana a shafin X cewa ta samu kiran neman agaji daga mutanen da ke cikin jirgin Freedom Flotilla.

“Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa, ciki har da na ruwa, su tallafa wa jirgin da ma'aikatansa kamar yadda ake bukata,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa: “Ina da tabbacin cewa hukumomin da suka dace za su binciki gaskiyar lamarin kuma su ɗauki matakin da ya dace.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#