Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Turkiyya ta shirya gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a fannin tsaro, sufurin jiragen sama, da fannonin fashahar kere-kere, yana mai cewa ƙwarewar Italiya da karfin samar da kayayyaki na Turkiyya na iya zama mai amfani a gare su, in ji Erdogan.

Erdogan ya yaba kakkarfar alakar Turkiyya-Italiya, ya yi nuni ga hadin kai a Afirka da fannin tsaro

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana aniyar Turkiyya ta zurfafa alaƙa da Italiya a ɓangarorin kasuwanci, da tsaro, da diflomasiyya, bayan wata babbar ziyara da ya kai Rome inda ƙasashen biyu suka gudanar da taron gwamnatoci karo na huɗu.

Da yake tattaunawa da ‘yan jaridu a cikin jirgin sama yayin komawa gida, Erdogan ya bayyana tafiyar a matsayin mai nasara da alfanu, yana mai karin haske kan yiwuwar aiki tare a Afirka, musamman a ɓangarorin tsaro da taimakon jin ƙai.

Ya haɗa gwiwa wajen jagorantar taron da Firaministar Italiya Giorgia Meloni tare da jaddada cewa gwamnatocin biyu sun amince da ɗaga martabar alaƙarsu ta kasuwanci daga dala biliyan 30 zuwa dala biliyan 40 a nan gaba kaɗan.

“Tun baya ma alaƙarmu da Italiya na kan kyakkyawar turba. Alaƙarmu ta tarihi, da amfani da teku guda, da haɗin kai mai zurfi, da buƙatu iri guda, da batutuwa da dama da muke da ra’ayi guda a kan su, duk na ƙarfafa gwiwowinmu wajen bunƙasa alaƙar. Shi ya sa muke da manufofi masu kyau da muke da burin cim ma wa.

Ya ƙara da cewa a yayin ziyarar an sanya hannu kan yarjeniyoyi 11.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#