Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban TEKNOFEST ya jaddada cewa AI na iya ba da damar yin sabbin abubuwa a fannin kiwon lafiya, samar da damammaki ta fannin ilimi, da damammaki marasa adadi da za su sauƙaƙa rayuwa.

Fasaha mai ƙarfi da ƙirƙirarriyar basira ne sabbin mabuɗan duniya — Shugaban TEKNOFEST

Shugaban baje-kolin fasaha na TEKNOFEST na Turkiyya, ya bayyana cewa amfani da fasaha da ƙirƙirarriyar basira su ne sabon mabuɗan duniya, inda ya jaddada cewa ƙirƙirarriyar basiya idan aka yi amfani da ita yadda ya dace, za ta taimaka wa bil’adama domin samun makoma mai kyau.

Selcuk Bayraktar, da yake jawabi a wurin bude taron TEKNOFEST TRNC, wanda aka gudanar a tsohon filin jirgin sama na Ercan da ke Lefkosa, ya jaddada cewa AI na iya ba da damar yin sabbin abubuwa a fannin kiwon lafiya, samar da damammaki ta fannin ilimi, da damammaki marasa adadi da za su sauƙaƙa rayuwa.

Yayin da yake la’akari da cewa duniya ta shiga cikin wani duhu, Bayraktar ya ce: "Babban laifi ga bil'adama, kisan kiyashi yana faruwa a kusa da mu, ana jefa bama-bamai a Gaza.

 “Wannan duhun za a iya cire shi ne kawai ta hanyar gaskiya. Duniya wadda za a yi amfani da fasaha domin tabbatar da adalci da samar da tausayi.”

Kan batun halin da ake ciki a Arewacin Cyprus ta Turkiyya, ya ce ƙasar ba wai za ta zama alama ta gwagwarmaya a tarihi ba, amma wadda ta samu manyan nasarori.

Ya kuma jaddada cewa, ya kamata ƙasar ta kasance cibiyar da ke da sha'awar fasaha da kimiyya a tsakiyar tekun Bahar Rum.

Ya jaddada cewa ya kamata a ziyarci TRNC ba don hutu kawai ba har ma da kimiyya, fasaha, da kuma ƙere-ƙere.

“TRNC tsibiri ne na zaman lafiya. Yana da tabbacin zaman lafiya da tsaro da ‘yan uwantaka a Bahar Rum.”

Cibiyar Fasaha ta Turkiyya (T3) Foundation da Ma'aikatar Masana'antu da Fasaha ta Turkiyya ne suka shirya TEKNOFEST, kuma ana gudanar da baje-kolin kowace shekara tun daga 2018 tare da tallafin hukumomin gwamnati da dama, abokan kamfanoni masu zaman kansu, da jami'o'i.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ci gaba da zama babban abokin shirin na TEKNOFEST ta ɓangaren watsa labarai.

Yayin da aka saba gudanar da bikin a garuruwa daban-daban na Turkiyya a shekarun wabi (misali shekarar 2018) da kuma birnin Istanbul a shekarun mara (misali shekarar 2019), TRNC ta kasance ƙasa ta biyu da ta ƙarbi baƙuncin taron a ƙetare bayan Azerbaijan, wadda ta karɓi baƙuncin TEKNOFEST a shekarar 2022.

A shekarar 2024, taron da aka yi a birnin Adana da ke kudancin Turkiyya ya samun halartar baƙi miliyan 1.1.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#