Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Taron na kwanaki huɗu ana yinsa ne a tsohon filin jiragen sama na Ercan a Lefkosa, babban birnin ƙasar, a ƙarƙashin ofishin shugabancin ƙasar TRNC, kuma ya tattara jerin gasa da bajekoli da kuma tarukan bita.
An buɗe taron TEKNOFEST TRNC na shekarar 2025 a Arewacin Cyprus na Turkiyya (TRNC), inda ya haɗa dubban masoya fasaha da masu ƙirƙira da kuma baƙi daga sassan duniya.
Taron na kwanaki huɗu,da aka fara ranar Alhamis, ana yinsa ne a filin tsohon jiragen sama na Ercan a Lefkosa, babbn birnin ƙasar, a ƙarƙashin jagorancin shugabancin TRNC, kuma ya ƙunshi jerin shirye-shirye na gasa da bajekoli da kuma tarukan bita.
Fiye da mutum 47,000 daga ƙasashe 22 ne suka nemi shiga jerin gasar wannan shekarar, da tawagogi 268 kuma mutum 1,083 ne suka samu suka kai ga zagaye na ƙarshen gasar. Cikin waɗanda suka kai ga zagaye na ƙarshen, 334 mata ne kuma 749 maza ne.
Jerin gasar na cikin muhimman matakai shida ne da kuma ƙananan matakai gasa 13, inda za a yi bajekolin ƙirƙire-ƙirƙire a fannin sufurin sararin samaniyya da mutum mutumi mai motsi da manhajoji da kuma fannoni na zamani.
Kamar yadda aka saba a ko wace shekara, TEKNOFEST TRNC tana da rumfunan shirye-shirye da talla masu yawa.
Taron TEKNOFEST na ƙetare na biyu
Akwai jumullar rumfuna 116, ciki har da rumfunan masu ruwa da tsaki 81 da kuma rumfuna 11 da kamfanoni da makaranti huɗu da suka shiga gasar da kuma rumfunan sayar da abinci 20.
A lokacin bikin bajekolin, za a yi atisayen nuna tashin jiragen sama na ƙasar, inda jiragen saman Bayraktar AKINCI da Bayraktar TB2 da HURKUS da ANKA da AKSUNGUR da Gendarmerie Steel Wings da ATAK helicopter da Turkish Stars da SOLOTURK da kuma jirage da dama da za su bajekolin tashinsu.
Taron TEKNOFEST da Gidauniyar Tawagar Fasaha ta Turkiyya (T3) da kuma ma’aikatar masana’antu da fasaha ta Turkiyya suka shirya, ana yin sa ne a ko wace shekara tun shekarar 2018 da tallafin gwamman ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu da kuma jami’o’i.
Yayin da ake yin taron a biranen Turkiyya dabandaban a shekarun wabi (misali shekarar 2018) da kuma birnin Istanbul a shekarun mara (misali shekarar 2019), TRNC ta kasance ƙasa ta biyu da ta ƙarbi baƙuncin taron a ƙetare bayan Azerbaijan, wadda ta karɓi baƙuncin TEKNOFEST a shekarar 2022.
A shekarar 2024, taron da aka yi a birnin Adana da ke kudancin Turkiyya ya samun halartar baƙi miliyan 1.1.
Comments
No comments Yet
Comment