Sport
Dollar
38,5681
0.32 %Euro
43,8973
0.77 %Gram Gold
4.038,3700
0.86 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Fahrettin Altun ya yaba wa TRT game da kasancewarta muryar Turkiyya a ƙasashen duniya, yana mai cewa ta zama wakiliyar ƙasar a fafutukarta wajen ganin an yi adalci a duniya da kuma tsinkayenta a fannin watsa labarai.
Shugaban Sashen Sadarwa na gwamnatin Turkiyya Fahrettin Altun ya miƙa saƙonsa na taya murna ga TRT a yayin da kafar watsa labaran ta gwamnatin ƙasar take bikin cika shekaru 61 da kafuwa, inda ya bayyana ta a matsayin babbar madogara a fafutukar Turkiyya ta fayyace gaskiya da alkinta tarihi da sadarwa ga duniya.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Altun ya jinjina wa TRT a matsayin “muryar ƙasarmu kuma abin alfaharunmu,” inda ya yaba mata saboda kwashe fiye da shekaru sitti tana watsa labarai da bauta wa al’umma.
“TRT ba kawai labarai ta kwashe shekaru aru-aru tana watsawa ba har ma da tsayin da ta yi wajen faɗin gaskiya da kasancewarwa wata gada da ke haɗa shugabanni da al’ummarsu,” in ji Altun.
Ya yaba wa kafar watsa labaran game da kasancewarta muryar Turkiyya a ƙasashen duniya, yana mai cewa ta zama wakiliyar ƙasar a fafutukarta wajen ganin an yi adalci a duniya da kuma tsinkayenta a fannin watsa labarai.
“A yau, TRT ba kafar watsa labarai ba ne kawai,” in ji Altun, “wata kafa ce ta sadarwa ta Turkiyya da ke bayar da fifiko wajen fayyace gaskiya da kare martaba, da yin komai bisa tsari.”
Ya bayyana muradin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na “Ƙarnin Turkiyya”,inda ya ƙara da cewa kafar watsa labaran tana taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa matsayin Turkiyya a ƙasashen duniya.
A wani ɓangare na tsarin sadarwa, Altun ya sha alwashin goyon bayan ci gaba da faɗaɗa TRT don ta ƙara ƙarfi a duniya.
Da yake kammala bayani, Altun ya gode wa ma’aikatan TRT na baya da na yanzu sannan ya yi fatan ci gaba da ƙara samun nasara a gare ta.
Comments
No comments Yet
Comment