Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A makon jiya, Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya shaida wa shugabannin sojoji cewa Boko Haram da ISWAP suna sake tattaruwa a tsibiran Tafkin Chadi, da dajin Sambisa da tsaunukan Mandara, sakamakon "koma bayan da sojoji suka samu".
Wasu ‘yan ta’adda da suke da alaƙa da ƙungiyar IS sun buɗe wuta kan masu zaman makoki a wani ƙauye a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, inda suka kashe mutane 15, kamar yadda wani jagoran al’umma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Talata.
Harin, wanda aka kai ranar Litinin, shi ne na baya bayan nan a jerin hare-hare a yankin, wanda ya ƙara ƙamari a ‘yan makonnin nan.
Fiye da mutane 50 aka kashe a makon jiya.
Mayaƙan ƙungiyar IS a Yammacin Afirka (ISWAP) sun afka wa ƙauyen Kwaple, kusa da ƙauyen Chibok, a kan babura da dama, inda suka buɗe wuta kan jama’ar da suke zaman makokin wani jagoran al’umma a ƙauyen, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.
“A safiyar yau, an gano gawawwaki 15 a ƙauyen da kuma dazukan da suke kewayensa, a cewar Ayuba Alamson, wani jagora a Chibok, kimanin kilomita 15 daga ƙauyen.
“Mayaƙan na ISWAP sun buɗe wa jama’a wuta, sannan suka bi waɗanda suka gudu cikin daji a kan babura,” a cewar Alamson.
ISWAP, wacce ta ɓalle daga Boko Haram a 2016, ta ƙwace dajin Sambisa a 2021 kuma ta ci gaba da kai hare-hare ƙauyukan da ke kusa da dajin.
A ranar Alhamis, Boko Haram ta kashe manoma 14 a Gwoza, kusa da kan iyaka da Kamaru, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
A makon jiya, Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya shaida wa shugabannin sojoji cewa Boko Haram da abokiyar adawarta ISWAP suna sake tattaruwa a tsibiran gefen Tafkin Chadi, da dajin Sambisa da tsaunukan Mandara a kan iyakar Kamaru, sakamakon “koma bayan da sojoji suka samu”.
Comments
No comments Yet
Comment