Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sojojin sun ce sun kashe Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji, da Kachallah Suza da wasu 'yan ta'adda da dama a samamen da suka kai Talata Mafara da Kaura Namoda.
Rundunar Sojin Nijeriya ta samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama a Jihar Zamfara, ciki har da wasu gawurtattu biyar da suka addabi al’umma.
Rundunar sojin ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda ta ce sojojin Brigade na 1 ne suka kai samame a Ƙananan Hukumomin Talata Mafara da Kaura Namoda.
“A ranar 1 ga watan Mayun 2025 da Asubahi, sojojin rukunin Combat 6 a lokacin da suke shawagi, sun rutsa da wasu ‘yan ta’adda masu ɗauke da muggan makamai waɗanda suka kai hari ƙauyen Kwanugga da ke Ƙaramar Hukumar Talata Mafara.
“'Yan ta'addan waɗanda suka tayar da tarzoma ta hanyar kai wa fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba hari tare da rusa gidajensu, an buɗe musu wuta yadda ya kamata. Wannan arangamar dai ta yi sanadin halaka ‘yan ta’addan da dama waɗanda suka haɗa da wasu manyan ‘yan bindiga biyar masu suna Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji, da Kachallah Suza,” kamar yadda sanarwar ta sojin ta bayyana.
Sojojin kuma sun ce dakarunsu sun bi sauran ‘yan ta’addan da suka tsere inda suka samu nasarar ƙwato makamai da dama daga hannunsu waɗanda suka haɗa da bindigogi ƙirar AK 47 da harsasai da makaman RPG da babama-bamansu.
Rundunar sojin ta yi godiya ga mazauna yankunan kan irin gudunmawar da suka bayar ta hanyar bayar da bayanan sirri kan lokaci wanda sojojin suka ce ya yi matuƙar taimaka musu.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ake fama da matsalar ‘yan fashin daji.
Ko a kwanakin baya sai da sojojin na Nijeriya suka samu nasarar kashe ‘yan fashin daji da dama a Zamfara ciki har da mai gidan su Bello Turji wato Halilu Sububu.
Sai dai a halin yanzu jama’ar yankin sun fi kiraye-kiraye kan a yi maganin Bello Turji sakamakon yadda shi da yaransa suke addabar ƙauyukan jihohin Zamfara da Sokoto.
Comments
No comments Yet
Comment