Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Mele Kyari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar bayan wata takarda mai tambarin hukumar EFCC ta rinƙa yawo a kafofin sada zumunta da kuma labaran da wasu jaridun ƙasar suka rinƙa ruwaitowa kan cewa an kama tsohon shugaban

Mele Kyari ya musanta rahotannin da ake yaɗawa kan cewa yana tsare a hannun EFCC

Tsohon shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPCL Mele Kyari ya yi watsi da rahotannin da wasu kafafen watsa labarai na ƙasar suka ruwaito kan cewa yana tsare a hannun hukumar EFCC.

Mele Kyari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar bayan wata takarda mai tambarin hukumar EFCC ta rinƙa yawo a kafofin sada zumunta da kuma labaran da wasu jaridun ƙasar suka rinƙa ruwaitowa kan cewa an kama tsohon shugaban da wasu muƙarrabansa da suka yi aiki tare.

Sai dai Kyari ya yi watsi da wannan batu inda ya ce bi-ta-da-ƙulli ce kawai ake masa da neman cim ma wata manufa.

“A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata musamman sa’o’i biyu da suka gabata, na ta samun kiraye-kirayen waya daga ‘yan uwa da abokai da suka shiga damuwa kan zargin da wata jaridar intanet ta yi kan cewa ina tsare a hannun hukumar EFCC.

“Wannan a bayyane take wani makirci ne da kuma rashin lissafi daga jaridar da masu ɗaukar nauyinta domin cim ma wata manufa, wadda su kaɗai suka sani,” kamar yadda Kyari ya bayyana.

Tshon shugaban na NNPCL ya kuma ce a halin yanzu yana hutu ne bayan an sauke ma’aikatan hukumar gudanarwa ta NNPCL wadda yake jagoranta.

Kyari ya kuma bayyana cewa ya yi aiki a hukumar tsawon shekara 34 kuma a tsawon shekarun da ya shafe musamman shekaru biyar na ƙarshe bai samu lokacin hutawa ba inda ya gode wa damar da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Shugaba Bola Tinubu suka ba shi.

“Dole ne na jaddada cewa na gudanar da aikina {na NNPCL} bisa tsoron Allah tare da kwana da sanin cewa a matsayina na Musulmi idan ban bayar da shaida a gaban ɗan’adam ba, zan bayar a gaban Allah,” kamar yadda Kyari ya bayyana.

 “Duk da haka, yana da muhimmanci a bayyana cewa dogara da labaran ƙarya ba zai amfanar da kowa da komai ba, ko ga NNPCL ko ƙasa baki ɗaya, inda hakan zai iya aika saƙo mara kyau ga masu son zuba jari da ƙasashen waje,” kamar yadda ya ƙara bayyanawa.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#