Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A karon farko, dakarun RSF sun kai hari wuraren da soji ke iko da su a Port Sudan da jirage marasa matuƙa masu ƙunar-baƙin-wake, wanda wata alama ce da ke nuna wani sabon salo da yaƙin ke ɗauka wanda aka shafe fiye da shekara biyu ana gwabzawa
Dakarun RSF na Sudan a ranar Lahadi sun kai hari a birnin Port Sudan, kamar yadda rundanar sojin ƙasar ta tabbatar.
Mai magana da yawun sojin Sudan Nabil Abdullah ya bayar da rahoton cewa ba a samu asarar rai ba, sai dai “lalata abubuwa ƙalilan” a birnin, da ke gaɓar Tekun Bahar Maliya ta Sudan.
Dakarun na RSF waɗanda ke yaƙi da sojojin na Sudan tun daga Afrilun 2023, na yawaita amfani da jirage marasa matuƙa a ‘yan kwanakin nan tun bayan da suka rasa wurare da dama da suke iko da su a ƙasar ciki har da sassan Khartoum babban birnin ƙasar a watan Maris.
Mai magana da yawun sojojin ƙasar Nabil Abdullah a wata sanarwa da ya fitar ya ce RSF ɗin ta kai hari “sansanin sojin sama na Osman Digna, da wani wurin ajiye kayayyaki da wani wurin farar-hula da ke birnin na Port Sudan ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi na ƙunar-baƙin-wake.”
Hotunan AFP sun nuna hayaki ya turnuƙe a kusa da filin jirgin da ke kudancin Port Sudan, mai nisan kilomita 650 daga wuri mafi kusa da wurin da mayaƙan RSF suke a gefen Khartoum.
A garin Kassala da ke kan iyaka da gabashin ƙasar, mai tazarar kilomita 500 kudu da Port Sudan, kusa da Eritrea, shaidun gani da ido sun ce jiragen sama marasa matuka uku ne suka kai hari a filin jirgin sama a ranar Lahadi a rana ta biyu a jere.
A garin Kassala da ke kan iyaka da gabashin kasar, mai tazarar kilomita 500 kudu da Port Sudan, kusa da Eritrea, shaidun gani da ido sun ce jiragen sama marasa matuka uku ne suka kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama ranar Lahadi a rana ta biyu a jere.
Wakilin AFP a Port Sudan ya ce gidansa da ke da tazarar kilomita 20 daga filin jirgin saman ya rinƙa girgiza yayin da aka ji ƙarar fashewar wasu abubuwa da sanyin safiyar Lahadi.
Wani fasinja ya shaida wa AFP daga filin jirgin cewa “muna hanyar zuwa wurin jirgi inda aka yi sauri aka kwashe mu daga wurin shiga jirgin”.
An dakatar da tashi da saukar jirage a Port Sudan, wanda nan ne wuri ɗaya kacal da ake shiga Sudan tun bayan soma wannan yaƙin.
Comments
No comments Yet
Comment