Dollar

38,5723

0.32 %

Euro

43,6631

0.24 %

Gram Gold

4.000,6200

-0.08 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Babu rahoto game da mutuwa ko jikkata sakamakon luguden wutar, wanda rundunar RSF ta yi, bayan wani irinsa da ta yi a hedkwatar bayar da umarni ta soji da ke Khartoum ranar 26 ga watan Afrilu.

Dakarun RSF sun yi luguden wuta a fadar shugaban ƙasar Sudan da ke Khartoum

Dakarun rundunar ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF) a Sudan sun yi luguden wuta a fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum a karo na biyu na irin wannan hari da suka kai a babban birni a ƙasa da mako ɗaya, a cewar wasu majiyoyi na soji.

Rundunar RSF ranar Alhamis ta harba makaman atilari masu cin dogon zango zuwa fadar shugaban ƙasar daga lardin Al Salha da ke tsallaken Kogin White Nile, wanda shi ne wuri mafi kusanci da fadar shugaban ƙasa da suke riƙe da shi tun bayan da sojojin gwamnati suka sake ƙwace Khartoum daga hannunsu a watan Maris, kamar yadda wata majiya da ba ta so a bayyana ta ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Babu rahoto game da mutuwa ko jikkata sakamakon luguden wutar, wanda rundunar RSF ta yi, bayan wani irinsa da ta yi a hedkwatar bayar da umarni ta soji da ke Khartoum ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Dakarun RSF da na gwamnati sun ƙaddamar da yaƙi da juna tun watan Afrilun 2023. Yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba mutum fiye da miliyan 13 da muhallansu.

An kashe farar-hula fiye da 500 a cikin mako uku a Sudan: MDD

Dakarun RSF sun mayar da hankali wajen ƙwace garuruwan da ke yammacin Darfur tun bayan da dakarun gwamnati suka ƙwace birnin Khartoum daga hannunsu a watan Afrilu, kuma babbar tungarsu ta ƙarshe da take hannun dakarun gwamnati shi ne birnin Al Fasher.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#