Dollar

38,5704

0.32 %

Euro

43,6689

0.25 %

Gram Gold

4.005,9300

0.05 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Babban jami'in kare haƙƙin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce, "Abin firgicin da ke faruwa a Sudan ba shi da iyaka”.

An kashe farar-hula fiye da 500 a cikin mako uku a Sudan: MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla fararen-hula 542 ne aka tabbatar an kashe su a yankin arewacin Darfur na kasar Sudan cikin makonni uku da suka gabata, inda ta yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu ya zarce haka.

Babban jami'in kare haƙƙin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce, "Abin firgicin da ke faruwa a Sudan ba shi da iyaka”.

Musamman yankin Darfur ya zama wani muhimmin fagen daga a yaƙin da ya ɓarke a ranar 15 ga Afrilun 2023 tsakanin rundunar ta yau da kullun ƙarƙashin jagorancin Abdel Fattah al Burhan, da kuma rundunar Rapid Support Forces (RSF), ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo.

Yakin ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da janyo abin da hukumomin agaji suka bayyana a matsayin yaƙi mafi girma da aka fi samun gudun hijira da matsalar yunwa a duniya.

Yakin El-Fasher, wanda shi ne babban birni na ƙarshe a Darfur da ya suɓuce daga hannun RSF, ya kara tsananta a 'yan makonnin da suka gabata, yayin da RSF ɗin ke neman biyan diyya kan asarar da suka yi a babban birnin kasar Khartoum a watan jiya.

Mista Volka ya yi nuni da wani harin da RSF ta kai kwanaki uku da suka gabata kan El-Fasher da kuma sansanin Abu Shouk wanda ya kashe fararen hula aƙalla 40.

“Wannan ya kawo adadin fararen hula da aka tabbatar da an kashe a Arewacin Darfur zuwa aƙalla 542 a cikin makonni uku kacal da suka wuce,” in ji shi, inda yake ganin cewa da alama wannan adadin ma ya fi haka.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#