Shugaban Amurka ya ce yana ganin zai yi aiki da 'yan Democrat sai in har sun zaɓi lalata lammura, yana mai ƙrawa da cewa yana da ikon hawa kujerar na-ƙi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar cewa 'yan Democrat za su iya yunƙurin tsige shi, bayan nasarar da suka samu a zaɓukan rabin wa'adi ranar Laraba.
Trump ya ce ko kaɗan bai damu da yiwuwar hakan ba, yana mai gargaɗin cewa yunƙurin tsige shi zai iya jefa jam'iyyar Democrat cikin matsalar siyasa.
Da yake magana a fadar White House a karon farko tun bayan bayyana sakamakon zaɓukan rabin wa'adin, Trump ya ce bai damu ko kaɗan da yiwuwar tsige shi ba.
“A'a, a'a, a'a, ko kaɗan,” in ji Trump lokacin da aka tambaye shi ko yana fargabar cewa 'yan Democrat za su yi yunƙurin tsige shi.
“Na yi imanin hakan zai zama babban kuskure ga jam'iyyar Democrat idan suka yi ƙoƙarin hakan, domin zai zama tsige mutum ba tare da wani dalili ba. A kan me? Saboda ƙoƙarin samar da ƙasa mai wadata?” in ji shi.
Hegseth yana “aiki mai kyau sosai”
Trump ya nuna cewa a shirye yake ya yi aiki tare da 'yan Democrat a Majalisar Dokokin Amurka, muddin ba su yi ƙoƙarin kawo cikas ga ayyukan gwamnatinsa ba.
“Zan iya yin aiki tare da 'yan Democrat, sai dai idan suka yi ƙoƙarin kawo cikas ga lamura. Amma ina da ikon amfani da kujerar na-ƙi,” in ji shi.
Trump ya kuma ce ba shi da shirin korar Ministan Tsaro, Pete Hegseth, duk da asarar da jam'iyyar Republican ta yi a zaɓukan rabin wa'adi, lamarin da ya janyo suka kan yadda gwamnatin ta tafiyar da yaƙin da ake yi da Iran.
“A'a, ina ganin yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata,” in ji Trump lokacin da aka tambaye shi ko yana tunanin sauya Hegseth, wanda ya yi kaurin suna wajen goyon bayan kai hare-haren soji kan Iran.
Kalaman Trump na zuwa ne bayan jam'iyyar Democrat ta samu gagarumar nasara a zaɓukan rabin wa'adi, inda ta ƙwace rinjaye a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, a wani sakamako da ya nuna yadda goyon bayan masu zaɓe ya karkata zuwa gare ta a faɗin ƙasar.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AP

