Sport
Dollar
38,6088
-0.02 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.018,8000
0.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ana sa ran shugabannin kasashen Afirka da dama ne za su halarci bikin rantsuwar wanda za a yi a filin wasa mai ɗaukar mutum 40,000 da ke arewacin babban birnin kasar Libreville.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Gabon Brice Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo ƙarshen mulkin iyalan Bongo na gomman shekaru, zai sha rantsuwar kama aiki bayan ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya ta watanni 19.
Ana sa ran shugabannin kasashen Afirka da dama ne za su halarci bikin rantsuwar wanda za a yi a filin wasa mai ɗaukar mutum 40,000 da ke arewacin babban birnin kasar Libreville.
Daga cikin shugabannin da ake sa ran za su halarci taron akwai Adama Barrow na Gambia, Bassirou Diomaye Faye na Senegal, Ismail Omar Guelleh na Djibouti da Teodoro Obiang Nguema Mbasogo daga Equatorial Guinea.
Haka shi ma Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai samu wakilcin mataimakinsa Kashim Shettima a wurin bikin rantsuwar.
A cewar kafafen yada labarai na cikin gida da na waje, shugaban Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo Felix Tshisekedi shi ma zai halarci taron tare da takwaransa na Rwanda Paul Kagame, wanda ma'aikatar harkokin wajen Kigali ta tabbatar da halartar sa.
A halin yanzu Kigali da Kinshasa suna tattaunawa don kawo ƙarshen faɗa a gabashin DRC.
An ba da kyautar tikitin halartar taron a filin wasa na Angondje, wanda aka gina don girmama abokantaka tsakanin Gabon da China, kuma wannan shi ne karon farko da kasar za ta gudanar da bikin ranstuwa a gabon ɗimbin jama’a haka
Baya ga rantsuwa, an shirya gudanar da wasu abubuwa na nishaɗi waɗanda suka haɗa da faretin soji.
Comments
No comments Yet
Comment