Dollar

38,5840

0.04 %

Euro

43,8210

0.41 %

Gram Gold

4.121,8200

2.56 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Za a rufe manhajar wadda mallakar kamfanin Microsoft ce a ranar Litinin 5 ga watan Mayu bayan ta shafe shekara 22 ana amfani da ita.

Kamfanin Microsoft zai rufe manhajar Skype bayan shafe fiye da shekara 22 tana aiki

Za a rufe manhajar Skype wadda ta shahara a shekarun baya wurin buga waya da aika saƙonni ta intanet.

Za a rufe manhajar wadda mallakar kamfanin Microsoft ce a ranar Litinin 5 ga watan Mayu bayan ta shafe shekara 22 ana amfani da ita.

Wasu injiniyoyi ne suka ƙaddamar da manhajar sannan kamfanin Microsoft ya saye ta daga baya a shekarar 2011.

A ranar 28 ga watan Fabrairun bana, Microsoft ya sanar da cewa zai kawo ƙarshen amfani da manhajar.

“Daga Mayun 2025, ba za a ci gaba da samun Skype ba,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sai dai kamfanin fasahar na Microsoft ya bayar da dama ga masu amfani da Skype ɗin su yi amfani da adireshinsu domin shiga sabuwar manhajar ta Microsoft, wato Microsoft Teams.

Sanarwar ta ce ta hanyar amfani da Teams, masu amfani da Skype ɗin a baya za su iya samun abubuwa iri ɗaya da suke amfani da su a Skype, waɗanda suka haɗa da kiran waya da aika saƙonni da kuma aika bayanai.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#