Sport
Dollar
40,5829
0 %Euro
47,2159
0.08 %Gram Gold
4.321,8800
-0.02 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Duk da cewa kusan mutum miliyan 10 na cikin hatsari, Google ya gaza fitar da ƙaƙƙarfan gargaɗinsa a lokacin da Turkiyya ta gamu da bala'i mafi muni a tarihinta na zamani.
Kamfanin Google ya amince cewa tsarinsa na Android da ke gargaɗi kan girgizar ƙasar, Android Earthquake Alerts, da ya ƙirƙira ya kasa isar da sahihin gargaɗi a kan lokaci ga miliyoyin mutane kafin girgizar ƙasa mai tsanani ta afku a Turkiyya a watan Fabrairu na shekarar 2023.
A ranar 6 ga Fabrairun 2023, girgizar ƙasa guda biyu masu ƙarfi da suka kai girman 7.7 da 7.6 sun kashe mutane sama da 50,000 tare da jikkata fiye da 100,000 a Turkiyya kawai.
A maƙwabciyarta Syria, mutum 6,000 sun rasa rayukansu. Jimillar mutane sama da miliyan 14 ne wannan bala’i ya shafa.
Duk da tsananin bala’in da kuma yadda aka ji tasirin girgizar ƙasar a jihohi 11 na Turkiyya da suka haɗa da Adana, Adiyaman, Diyarbakir, Elazig, Hatay, Gaziantep, Kahramanmaras, Kilis, Malatya, Osmaniye da Sanliurfa – mutum 469 kawai tsarin na Google ya aika wa gargaɗinsa na gaggawa, na ɗaukar mataki.
Mutum kusan miliyan 10 ne suke zaune a nisan tazarar mil 98 (kilomita 160) daga ainihin inda girgizar ƙasa ta farko ta afku, wadda ta faru da misalin ƙarfe 4:17 na safe agogon ƙasar.
Gargaɗin mafi ƙarfi, wanda aka tsara shi ta yadda ko ka saita wayarka a “Do Not Disturb” tare da yin ƙara mai ƙarfi, ka iya ankarar da wadannan mutanen sakan 35 gabanin faruwar abin.
Amma, kusan mutane rabin miliyan ne kawai suka samu gargaɗin “Be Aware” wato “Yi Hankali,” wanda aka tsara don girgizar ƙasa marar ƙarfi kuma ba ya aiki idan aka saka “Do Not Disturb”, kamar yadda Google ya shaida wa BBC.
A irin wannan lokacin na safe, akwai yiwuwar mutane da yawa ba su ga wannan gargaɗin ba.
Da farko, Google ta ce tsarin ya “yi aiki da kyau.” Amma bayan bincike na ciki da kuma matsin lamba, kamfanin ya amince cewa tsarin ya yi ƙasa a gwiwa wajen tantance ƙarfin girgizar ƙasa da kuma kasa aika gargaɗin da ya dace.
Tsarin Android Earthquake Alerts (AEA), wanda aka ƙaddamar a shekarar 2020 tare da haɗin gwiwar Hukumar Nazarin Girgizar Ƙasa ta Amurka, yana amfani da na’urorin motsi a cikin wayoyin Android don gano motsin ƙasa.
Idan na’urori da yawa a wani yanki suka gano motsi, tsarin yana tabbatar da bayanan kuma yana aika gargaɗi ga masu amfani da ke kusa.
Gargaɗin mafi girma, na “Take Action” wato “Ɗauki Mataki,” an tsara shi don girgizar ƙasa mai haɗari, yayin da ƙaramin gargaɗi na “Be Aware” wato, “Yi Hankali,” aka tanade shi don girgizar ƙasa mai sauƙi.
Tsarin yana aiki a kasashe kusan 100 kuma yana taka muhimmiyar rawa musamman a yankunan da girgizar ƙasa ke yawan faruwa kamar Turkiyya, inda na’urorin Android suka mamaye fiye da kashi 70 cikin 100 na kasuwar wayar hannu.
Bincike na ciki ya bayyana cewa AEA ya fara tantance girgizar ƙasa ta farko a matsayin mai girman 4.5 zuwa 4.9, wanda ya yi ƙasa da ainihin ƙarfinta.
Masu binciken Google sun bayyana wannan a matsayin sakamakon iyakokin dabarun gano su.
Girgizar ƙasa ta biyu da ta faru daga baya a ranar ita ma ba a ƙimantata da kyau ba: an aika gargaɗin “Dauki Mataki” guda 8,158 kawai, tare da kusan miliyan huɗu na gargaɗin “Yi Hankali.”
Google ta bayyana wahalar ƙimanta girman girgizar ƙasa a ainihin lokacin a cikin wani rubutu da ya wallafa a intanet.
“Ɗaya daga cikin mafi wahalar sassan tsarin EEW shi ne tantance girman girgizar ƙasa a ainihin lokacin,” in ji kamfanin.
“Samun wannan daidai yana da matuƙar muhimmanci – idan aka yi ƙasa da kimanta, za ka iya kasa gargaɗi ga mutanen da ke cikin haɗari; idan aka yi sama da kimanta, za ka iya aika gargaɗin ƙarya wanda zai rage amincewar jama’a.”
Bayan wannan kuskuren, injiniyoyin Google sun sabunta dabarun kuma sun yi kwaikwayon wannan lamarin.
Sabon tsarin ya samar da gargaɗin “Dauki Mataki” miliyan 10 da kuma gargaɗin “Yi Hankali” miliyan 67, wanda ya nuna yadda abubuwa za su iya kasancewa daban.
“Muna ci gaba da inganta tsarin bisa abin da muke koya daga kowace girgizar ƙasa,” in ji Google.
Comments
No comments Yet
Comment