Dollar

38,6020

0.02 %

Euro

43,9502

0.05 %

Gram Gold

4.134,8100

0.02 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bankin Duniya ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta aiwatar da sauye-sauyen da za su kare talakawan kasar daga raɗaɗin hauhawar farashin kayayyaki.

Bankin Duniya ya nemi gwamnatin Nijeriya ta kare talakawa daga hauhawar farashi

Bankin ya kuma shawarci gwamnati da ta inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyar samar da ayyuka masu inganci, wanda a cewarsa shi ne hanyar kawar da talauci.

Bankin Duniya ya bayyana hakan ne a cikin sabon rahoto na baya bayan nan na watan Afrilun 2025 na Talauci da Daidaito a Nijeriya, wanda aka sake a ranar Litinin.

A farkon watan da ya gabata ne bankin a cikin rahotonsa na Pulse na Afirka, ya bayyana cewa karin ‘yan Nijeriya za su zama matalauta a cikin shekaru biyar masu zuwa, inda ya yi nuni da raunin tsarin tattalin arzikin Nijeriya da dogaro da kudaden shigar man fetur, da kuma gazawar kasa a matsayin muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga rage radadin talauci.

Domin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki a kan talakawa da sauye-sauye na baya bayan nan da take yi, gwamnati ta kaddamar da bai wa iyalai miliyan 15 tallafin kudi na wucin gadi.

Sai dai kuma Bankin Duniyar ya ce ana samun tafiyar hawainiya a wajen rabon.

Bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki masu tsauri kamar cire tallafin man fetur da kuma sakin naira don kasuwa ta yi halinta.

Sauye-sauyen sun kara ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki.

Karuwar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru kaɗan zuwa kashi 24.23 a cikin Maris ɗin 2025, daga kashi 23.18 cikin ɗari a watan da ya gabata, wanda ya kasance mafi ƙaranci tun watan Yuni 2023.

Bankin Duniya ya ce, “Abubuwa marasa daɗi masu yawa a cikin yanayin rashin tsaro na tattalin arziki sun kara tabarbarewa da kuma ta’azzara fatara. Tun daga shekarar 2018/19, karin mutane miliyan 42 sun fada cikin talauci, don haka sama da rabin ‘yan Nijeriya (kashi 54) an kiyasta za su kasance cikin talauci a shekarar 2024, bisa hasashen Bankin Duniya.

"Duk da cewa sauye-sauyen da aka yi a baya bayan nan a fannin tattalin arziki sun fara daidaita tattalin arzikin kasar, amma hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da karuwa, inda hakan ke kawo cikas ga bukatun masu amfani da kayayyaki, da kuma ci gaba da yin illa ga karfin sayayya ta 'yan Nijeriya.

“Kudaden da ma'aikata ke samu bai ƙaru ba idan aka yi la’akari da hauhawar da ake samu, lamarin da ya jefa 'yan Nijeriya da dama, musamman a birane cikin talauci."

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#