Dollar

38,6475

0.03 %

Euro

44,0433

0.08 %

Gram Gold

4.266,4400

0.03 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hukumar ta ce mai fafatukar ya “ƙi zuwa duk da jerin saƙonnin gayyata da aka tura masa ta sanannen adireshinsa da kuma hanyar sadarwarsa.

Doka ta ba mu damar tsare Very Dark Man — EFCC

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa (EFCC) ta tabbatar da kama shararren mai fafatukar nan, Martins Vincent Otse, wanda ka fi sani da VeryDarkMan (VDM).

EFCC a wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, ta ce an kama Otse ne bayan an kai ƙararsa ga hukumar kan munanan zarge-zargen yin ba daidai ba game da kuɗi.

Ta ce mai fafatukar ya “ƙi ya bayyana a gaban hukumar duk da jerin goron gayyata da aka tura masa ta sanannen adireshinsa da kuma hanyar sadarwarsa”.

“Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin aiziƙin Nijeriya ta’annati,  EFCC, a ci gaba da sauƙe nauyin da ya rataya a kanta na yaƙar laifukan tattalin arziƙi da kuɗi, ta gayyaci Martins Vincent Otse saboda wasu jerin ƙararrakin da suka shafi batutuwa na zargin laifukan kuɗi a kansa,” in ji hukumar.

“Ya ƙi ya bayyana duk da jerin goron gayyata da aka tura masa ta hanyar sanannen adireshinsa da kuma hanyoyin tuntuɓarsa.

“Ƙararrakin sun danganci munanan zarge-zarge na yin ba daidai ba da kuɗi wanda hukumar ba za ta iya watsi da shi ba,” in ji ta a wata sanarwar da ta yi wa taken, “Tuhumar da EFCC ke yi wa Martins Vincent Otse”.

Hukumar EFCC, ta kuma ce saɓanin ƙorafin da mutane ke yi game da kama da kuma tsare Otse, hukumar tana da ‘yancin iya tsare shi.

Sai dai kuma ta ce an ba da belin mai fafatukar kuma za a sake shi bayan ya cika dukkan sharruɗan belin.

“Ya kamata a amince cewa hukumar tana sane game da sukar da wanda ake zargin ke yi kan harkokin ayyukan hukumar.

“Duk da cewa irin waɗannan ayyukan ababuwan Allahwadai ne, kamen da aka yi masa ba shi da alaƙa da irin waɗannan sukar. Za a bai wa hukumomin da suka dace su yi duba game da waɗannan matakan [sukar],” in ji hukumar.

A ranar Litinin ne wasu masu fafatuka suka bazama kan titunan Abuja inda suka yi ta zanga-zangar neman a saki VDM baya ga kiraye-kiraye da ake yi kan kafafen sada zumunta don neman a saki mai fafatukar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#