Sport
Dollar
38,7786
0.39 %Euro
43,8944
0.27 %Gram Gold
4.147,5900
1.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sahun farko na maniyyata 315 waɗanda suka kama hanyar ƙasa mai tsarki sun fito ne daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa inda jirgin Air Peace ne ya kwashe su.
Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ƙaddamar da tashin maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin 2025.
Shettima ya ƙaddamar da tashin maniyattan ne a filin jirgin Sam Mbakwe da ke birnin Owerri na Jihar Imo.
Sahun farko na maniyyata 315 waɗanda suka kama hanyar ƙasa mai tsarki sun fito ne daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa inda jirgin Air Peace ne ya kwashe su.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Farfesa Abdullahi Usman da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III da sauran manyan jami’an gwamnatin Nijeriya ne suka tarbi Kashim Shettima domin ƙaddamar da tashin maniyyatan.
Aƙalla mutum 43,000 ne waɗanda suka yi rajistar gudanar da aikin hajji daga jihohi da birnin tarayyar ƙasar za su tafi ƙasa mai tsarki domin sauke farali.
Hukumar alhazan ta ce jirgin Air Peace zai kwashi maniyyata 5,128 daga Jihohin Abia da Akwa Ibom da Anambra da Bayelsa da Benue da Cross River da Delta da Ebonyi da Edo da Ondo da Ribas da Taraba.
Sai kuma jirgin FlyNas zai ɗauki maniyyata da 12,506 daga Abuja babban birni Nijeriya da Kebbi da Legas da Ogun da Osun da Sokoto da Zamfara.
Sannan kuma jirgin Max Air zai ɗauki fasinjoji 15,2043 daga Jihohin Gombe da Jigawa da Kano da Katsina da Kwara da Oyo da Filato.
Comments
No comments Yet
Comment