Dollar

38,7684

0.01 %

Euro

43,0059

-1.51 %

Gram Gold

4.020,0000

-2.98 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Dubban ‘yan Nijeriya da dama ne ke tafiya ci-rani musamman zuwa ƙasashen Turai domin neman rayuwa mai kyau.

Gwamnatin Nijeriya za ta mayar da mutum 15,000 da suka maƙale a ƙasashen waje cikin ƙasar

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana tattaunawa kan yadda za a mayar da ‘yan ƙasar kimanin mutum 15,000 da suka maƙale a ƙasashen Kamaru da Nijar da Chadi da sauran sassan duniya cikin Nijeriya a cikin aminci.

Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan ci-rani da Waɗanda Suka Rasa Muhallansu, Alhaji Tijani Ahmed ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito.

Ahmed ya bayyana cewa akwai aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan shida da suka rasa muhallansu a cikin ƙasar, sannan akwai dubban ‘yan gudun hijira ‘yan Nijeriya da ke rayuwa a sassan duniya.

“Muna da ‘yan Nijeriya 15,000 da suke son komawa ƙasar don raɗin kansu; kuma muna da aƙalla mutum 100,000 da ke zaune a ƙasar nan a matsayin ‘yan gudun hijira.

“Duka waɗannan haƙƙinsu ya rataya ne a kan hukumar, domin ta taimake su,” kamar yadda ya bayyana.

Dubban ‘yan Nijeriya da dama ne ke tafiya ci-rani musamman zuwa ƙasashen Turai domin neman rayuwa mai kyau.

Sai dai akasari masu tafiyar sun ratsawa ta sahara ne da kuma ƙoƙarin bi ta teku domin tsallakawa zuwa Turai.

Mutane da dama na mutuwa a yayin wannan tafiya, wasu kuma idan sun je sukan maƙale su rasa wata madafa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#