Sport
Dollar
38,7999
0.05 %Euro
43,1640
0.17 %Gram Gold
4.035,9200
0.02 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tawagar ƙwallon Nijeriya ta 'yan ƙasa da shekaru 20 ta doke ta Senegal a wasan kwata-fainal na kofin Afrika na CAF U20 da ke gudana a Masar, inda kuma ta cancanci zuwa gasar duniya ta FIFA U20.
Tawagar ƙwallon Nijeriya, Flying Eagles ta samu nasarar wucewa matakin dab da na ƙarshe a gasar matasa ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta Afrika, CAF U20 da ke gudana a Masar.
Nijeriya ta doke Senegal, wadda ke riƙe da kofin da ci 3-1 a bugun fenareti, bayan an kammala wasa ba tare da wani ya ci ƙwallo ba.
A Litinin 12 ga Mayu ne aka buga wasan da ya ɗauki mintuna 120, a filin wasa na Suez Canal Stadium.
Tun a zagayen ‘yan rukuni, ba a taɓa doke tawagar Nijeriya ba.
Cancantar gasar duniya
‘Yan wasan Nijeriya Precious Benjamin, da Emmanuel Chukwu da Israel Ayuma ne suka ci ƙwallayen 3.
Ita kuwa Senegal, ta gaza cin ƙwallo karo uku, ta hannun Pierre Dorival’s, da Mame Mor Faye, da Ousmane Konaté.
Ɗan wasan Senegal Seydi Diouck ne ya ci ƙwallo ɗayar, wadda ta gaza yin tasiri wajen ba su nasara.
Wannan nasara na nufin tawagar Nijeriya za ta shiga sawun waɗanda za su wakilci nahiyar Afrika a gasar kofin duniya ta matasa ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta FIFA.
Gasar duniyar ta matasa za ta gudana ne a Chile, daga Satumba zuwa Oktobar 2025.
Comments
No comments Yet
Comment