Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Tauraron ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan shekara a Ingila, wanda Ƙungiyar Marubuta Wasanni ta Ingila ta zaɓa a bana.

Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon shekara a Ingila karo na 3

Ƙungiyar Marubuta Wasanni ta Ingila ta ayyana Mohamed Salah na Liverpool a matsayin gwarzon ɗan wasan shekara na kakar 2024/25, ɓangaren maza.

Salah, wanda ɗan asalin Masar ne, ya lashe kyautar a karo na uku, inda ya cim ma yawan lashe kyautar daidai da toshon ɗan wasan Arsenal, Thierry Henry.

Ƙungiyar marubutan ta kuma zaɓi tauraruwar ‘yar wasar ƙungiyar mata ta Arsenal, Alessia Russo a matsayin gwarzuwar shekara a bana.

Mohamed Salah ya samu ƙuri’u kashi 90 cikin 100, daga jimillar ƙuri’un da mambobinta 900 suka kaɗa.

Baya ga jagorantar Liverpool wajen lashe kofin Firimiya a karo na 20, Salah ya ci ƙwallaye 28 da tallafin ƙwallo 18.

Tsaffin gwarazan ‘yan wasa, Andy Cole da Alan Shearer su ne kawai suka kafa tarihin lashe kyautar marubuta wasannin har sau huɗu.

Tuntuni dai Liverpool ta lashe kofin Firimiya, amma akwai ragowar wasanni uku kafin kammala kakar ta bana, inda Mohamed Salah ke da damar ƙara bajintarsa a wajen cin ƙwallaye.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#