Sport
Dollar
38,7786
0.39 %Euro
43,8944
0.27 %Gram Gold
4.147,5900
1.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Haziƙin ɗan ƙwallon ƙafar Sifaniya, Lamine Yamal, wanda tauraruwarsa ke haskawa a ƙungiyarsa ta Barcelona da tawagar Sifaniya, ya bayyana sha'awarsa ta buga wasa a Ingila.
Ta bayyana cewa matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal yana sha’awar buga ƙwallon ƙafa a Ingila, kuma ya faɗi ƙungiyoyin da zai so a ce ya buga wa wasa watan wata rana.
Yamal, wanda ɗan asalin Sifaniya ne wanda tauraruwarsa ke haska wa a Barca da tawagar ƙasarsa Sifaniya, ya jinjina wa wasu matasan ‘yan wasa masu nuna gwaninta a halin yanzu.
Ya nuna cewa ɗan wasan Arsenal, Bukayo Saka yana burge shi, sannan ya faɗi ƙungiyoyi biyu da zai so a ce ya taka leda a can.
Yamal yana da shekaru 17 kacal a duniya, amma tuni ya fara kafa tarihi a fannin bajintar taka ƙwallo, da iya yanka, da cin ƙwallaye a manyan wasanni, gida da waje.
Hasali ma, tuni ya zama fuskar ƙwallo a Sifaniya, inda har ya fara bin sawun gwarzon ɗan wasan duniya da ya yi suna a Barcelona, Lionel Messi.
Barca dai na jiran bazara mai zuwa lokacin da Lamine yamal zai cika shekara 18 a duniya, domin ta ba shi kwantiragi mai tsawo, bayan da suka ƙi sauraron tayin sayan sa daga wasu ƙungiyoyin Turai.
Ra’ayin Yamal
An tambayi Lamine Yamal wa ye gwanin ɗan wasansa ban da ‘yan wasan Barcelona, sai ya ce, "A halin yanzu, a wajen Barca, ina ganin [Ousmane] Dembele ko Bukayo Saka suna nuna bajinta matuƙa."
Ya ci gaba da magana kan ƙungiyoyin da zai yi fatan buga wa wasa, inda ya ce, “Akwai su da dama da zan so na buga wa, musamman a wajen Turai. A Turai dai, fitattu waɗanda zan so na buga wa su ne Old Trafford da Anfield."
A yanzu dai, Yamal na shiryawa wasan Clasico da Barcelona za su yi da Real Madrid ran Lahadi 11 ga Mayu, inda ake ganin nasarar Barca za ta kai ta dab da lashe kofin LaLiga na kakar 2024-25.
Baya ga fagen ƙwallo, Lamine Yamal ya kama matakin gwarazan ‘yan wasannin motsa jiki na duniya irin su Messi, da Erling Haaland, da LeBron James, inda ya zama jakadan kamfanin Beats by Dr Dre, don tallata kayan jin kiɗa.
Comments
No comments Yet
Comment