Dollar

38,7727

0.03 %

Euro

43,1453

-1.16 %

Gram Gold

4.028,0300

-2.79 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An kashe mutum takwas a Ukum, tara a Logo da ke maƙwabtaka, sai kuma mutum uku-uku a Guma da Kwande, in ji ƙungiyar Red Cross a Jihar Benue.

An kashe mutum 23 a wani harin 'yan bindiga a Jihar Benue ta Nijeriya

Wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 23 a wasu hare-hare daban-daban a Jihar Benue da ke tsakiyar Nijeriya, kamar yadda wani jami’in kungiyar agaji ta Red Cross ya bayyana a ranar Lahadi sakamakon wata tarzoma a yankin. Hare-haren sun faru ne a daren Asabar a kauyuka hudu.

Rikici tsakanin makiyaya da manoma kan amfani da filaye ya zama ruwan dare a tsakiyar Nijeriya.

“Rahotanni daga wuraren sun tabbatar da kashe aƙalla mutum 23 daga hare-hare daban-daban,” kamar yadda sakataren ƙungiyar Red Cross a Benue Anthony Abah ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

An kashe mutum takwas a Ukum, tara a Logo da ke maƙwabtaka, sai kuma mutum uku-uku a Guma da Kwande, in ji shi, yana mai ruwaito alƙaluman daga jami’an da ke sa ido kan afkuwar bala’i na ƙungiyar.

Ya kara da cewa wasu da dama sun samu raunuka.

Rikici kan gonaki

Zuwa yanzu dai ‘yan sandan ƙasar ba su fitar da sanarwa.

Wasu daga cikin sabbin hare-haren an kai su ne a yankunan da an kai wasu hare-haren a watan da ya gabata, inda aƙalla mutum 56 suka mutu.

Hare-hare biyu da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai a farkon watan Afrilu a jihar Filato mai makwabtaka da jihar ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 100.

Ana yawan samun rikici kan gonakin da manoma da makiyaya ke amfani da su sakamakon sauyin yanayi da kuma ƙaruwar jama’a.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#