Dollar

38,7658

0.01 %

Euro

43,1122

-1.25 %

Gram Gold

4.033,9000

-2.65 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Fahrettin Altun ya jinjina wa haɗin kan ƙasa, ya girmama waɗanda suka yi shahada, kuma ya nuna yadda ƙasar ta duƙufa wajen samar da zaman lafiya da daidaituwar lamura, yayin da Turkiyya ta cim ma wani muhimmin mataki a yaƙin da take yi da ta'addanci.

Altun ya ce rusa PKK ya nuna cewa fatan Turkiyya na kawar da ta'addanci yana samun nasara

Matakin Turkiyya na kawar da ta’addanci na ƙara ƙarfi yayin da ƙasar ke shiga wani sabon shafi mai muhimmanci a ƙoƙarinta na yaƙi da ta'addanci.

Shugaban Sashin Sadarwa na Turkiyya, Fahrettin Altun, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Litinin cewa sanarwar da PKK ta yi ta ajiye makamai da rusa kanta alama ce a fili ta ci-gaban da aka samu ƙarƙashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Altun ya bayyana cewa wannan ci-gaba yana nuna mataki mai muhimmanci a tsarin “Turkiyya Da Babu Ta'addanci,” yana ƙarfafa ƙudurin ƙasa wanda ya jagoranci wannan mataki.

“Turkiyya ta yi sadaukarwa sosai a tsawon fiye da shekaru 40 ana rikici,” in ji shi, “ta biya farashi mai tsada, ta yi fama da wahalhalu, kuma abu mafi raɗaɗi, ta rasa ɗaruruwan 'ya'ya maza da mata a hidimar ƙasa.”

Ya ƙara da cewa: “Yayin da muka kai wannan muhimmin lokaci, muna tuna shahidanmu masu daraja da girmamawa, da tausayawa, da godiya — domin sadaukarwarsu ce ta kai mu wannan matsayi.”

Zaman lafiya, kwanciyar hankali, da adalci

Altun ya bayyana a fili cewa tsarin “Turkiyya Babu Ta'addanci” ba wani shiri ne na ɗan lokaci ba kuma ba wanda za a kammala cikin dare ɗaya ba. Maimakon haka, yunƙuri ne na dogon lokaci wanda aka gina bisa burin ƙasa na tabbatar da yanayin zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da rashin tashin hankali ga duk 'yan ƙasa.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin Turkiyya, tare da duk ƙwarewarta, da ƙarfin ta, da iliminta na cibiyoyi, za ta ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da cewa zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da adalci sun yi nasara.

Don tabbatar da ci gaba mai kyau na wannan tsari, Altun ya ce za a ɗauki matakan da suka dace kuma za a bi kowane mataki da gaskiya, da kulawa, da kyakkyawar manufa

“Za a aiwartar da matakan da ƙasarmu take ɗauka da matuƙar taka-tsantsan kuma a fayyace,” in ji shi. “Duk matakin da za a ɗauka zai zama na musamman kuma mai ƙarfi, don tabbatar da cewa tsarin ya ci gaba ba tare da tsaiko ba.”

Jagorancin Shugaba Erdogan

Altun ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan al'ummar Turkiyya, yana cewa: “Al'ummarmu masu daraja suna ci gaba da kasancewa tare da ƙasarmu, da gwamnati, da ƙaƙƙarfar manufar Shugabanmu — suna nuna goyon bayansu a kowane lokaci.”

Yayin da yake bayani kan yanayin haɗin kai da haɗin gwiwar tsarin, Altun ya yaba da kiran Shugaban Jam’iyyar MHP Devlet Bahceli na fara wannan matakin kuma ya yaba da jagorancin Shugaba Erdogan wajen aiwatar da shi.

“Wannan tafiya ce zuwa samar da Turkiyya da Babu Ta'addanci — tafiya da ake yinta da haɗin kai tsakanin gwamnati da al'umma, wajen gudanar da ita,” in ji shi.

Altun ya kammala da bayyana fatan cewa wannan tsari zai kawo zaman lafiya mai ɗorewa da sakamako masu kyau ba kawai ga Turkiyya ba, har ma ga yankin gaba ɗaya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#