Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya, Cevdet Yilmaz, ya ce dole ƙasashen Musulmai su ɗauki tsattsauran mataki kan ta’asar Isra’ila, tare da tallafa wa Falasɗinawa ta hanyar ɗaukar matakai na zahiri.

Dole ƙasashen Musulmai su tsaya tsayin daka kan ta’asar Isra’ila a Falasɗinu, in ji Turkiyya

Dole ƙasashen musulmai su tsaya tsayin daka kan mummunar ta’asar Isra’ila tare da goyon bayan Falaɗinu ta hanyar ɗaukar ƙwararan matakai, a cewar mataimakin shugaban ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz.

Yilmaz ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da yake jagorantar zaman rufe taron Kwamitin Haɗin Kan Tattalin Arziki da Kasuwanci na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai (OIC), wato COMCEC karo na 42, a Cibiyar Taro ta Istanbul.

"Duk da sanarwar tsagaita wuta, gwamnatin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na ci gaba da kisan gilla bisa dalilai marasa tushe, tare da hana kai agajin jinƙai da kuma ƙin zuwa mataki na gaba na yarjejeniyar tsagaita wutar," in ji shi.

A cewarsa, waɗannan matakai na ƙara tsananta wahalhalun da al’ummar Falasɗinu ke fuskanta a kullum.

“Dole mu, a matsayinmu na ƙasashen Musulmai, mu tsaya tsayin daka wajen adawa da wannan zalunci, tare da tallafa wa Falasɗinu, musamman Gaza, ta dukkan hanyoyin da muke da su, ta hanyar ɗaukar matakai na zahiri,” in ji Yilmaz.

Ya ce taron na COMCEC ya nuna aniyar ƙasashen Musulmai ta shawo kan rikice-rikicen siyasa da na tsaro da ke addabar duniyar Musulunci ta hanyar diflomasiyya.

Yilmaz ya kuma yi nuni da shirin Al-Quds na COMCEC a matsayin wata alama ta zahiri ta haɗin kai, inda ya bayyana cewa an ƙaddamar da sabbin ayyuka 10 a wannan shekara, baya ga 28 da aka riga aka kammala domin tallafa wa Falasɗinawa.

Haka kuma, ya yi maraba da ci gaban da aka samu ƙarƙashin shirin Syria na COMCEC, wanda aka aiwatar a wannan shekara domin ƙarfafa ƙwarewar mutane da cibiyoyi, tare da farfaɗo da harkokin tattalin arziki ta hanyar ayyuka biyar da ake gudanarwa

A ɓangaren tattalin arziki, Yilmaz ya sake jaddada burin OIC na ƙara yawan cinikayya tsakanin ƙasashe mambobinta zuwa kashi 25 cikin 100 na jimillar cinikayyarsu.

Ya ce faɗaɗa tsarin fifita cinikayya tsakanin ƙasashen OIC, tare da haɗa ayyuka da zuba jari da kasuwanci na zamani da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci, zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwa.

Ya ƙara da cewa zaman musayar ra’ayoyin ministoci na wannan shekara ya mayar da hankali kan samar da ingantattun hanyoyin samar da kuɗaɗen kasuwanci domin bunƙasa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, musamman ga ƙananan masana’antu da matsakaitan ’yan kasuwa.

Ya bayyana fatan cewa tattaunawa kan lamunin fitar da kayayyaki da tsarin ɗaga kafa wajen biyan kuɗi da inshora, da ana samar da kayayyaki, da kuma hanyoyin hada-hadar kuɗi za su buɗe ƙofa ga sabbin haɗin gwiwa.

Domin samar da yanayi mai inganci da tabbaci ga ’yan kasuwa, Yilmaz ya yi kira da a ƙarfafa hukumar cibiyoyin Sasanta Rikice-rikicen Kasuwanci ta OIC, domin warware takaddamar kasuwanci da zuba jari cikin sauri da adalci.

Ya kuma buƙaci a gaggauta soma gudanar da shirin Shaidar Halal na Musulunci, bisa Ƙa’idoji da Ma’aunin Ƙasashen Musulmai, domin sauƙaƙa amincewa da takardun shaidar halal tsakanin ƙasashe da kuma kawar da shingayen kasuwanci.

Yilmaz ya ce a ƙarƙashin tsarin tallafin ayyukan COMCEC, ana gudanar da ayyuka 31 a wannan shekara a fannoni da suka haɗa da ilimi da haɗin gwiwar fasaha da ƙwarewa na zamani tare da bunƙasa cibiyoyi.

Ya bayyana cewa jimillar ayyukan da shirin ya tallafa wa tun daga shekarar 2013 sun kai 209, inda dukka ƙasashe mambobin ƙungiyar suka samu halarta.

A cewarsa, ƙasashe 24 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 12 sun yi zaman tattaunawa kusan 62 a tsakaninsu a gefen taron.

Yilmaz ya sanar da cewa zaman musayar ra’ayoyin ministoci na shekara mai zuwa zai mayar da hankali kan amfani da hanyoyin kuɗi na Musulunci don tabbatar da wadatar abinci, yana mai bayyana batun a matsayin muhimmi ga manufofin ci gaban ƙasashe mambobin ƙungiyar.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Anadolu Ajansı

#