Sport
Dollar
38,7776
0 %Euro
43,3029
0.61 %Gram Gold
4.043,5400
0.2 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wani babban jami'in soja ya ce sama da sojoji 10 aka kashe a hari na biyu da aka cikin makonni biyu.
‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari wani sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Marte ta jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya, inda suka kashe wasu sojoji.
Majiyoyin soji sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa harin ya auku ne a sansanin Forward Operating Base na bataliya ta musamman ta 153 da misalin ƙarfe uku na daren Litinin.
Wani babban jami’in soji ya ce sama da sojoji 10 aka kashe a harin.
“‘Yan ta’addan sun mamaye Marte cikin tsakar daren jiya. Sama da sojoji 10 aka kashe kuma ɗaruruwan jami’ai sun arce. Sun [‘yan ta’addan] ƙona motoci masu sulke kuma sun tsere da makamai da harsasai,” in ji wata majiya.
Jami’an sojin Nijeriya ba su yi tsokaci a hukumance game da lamarin ba tukunna. Onyechi Anele, mai magama da yawun sojin Nijeriya, ya ce ana kan bincike yayin da aka fitar da wannan rahoton.
An kashe ‘yan Boko Haram da dama
Wannan shi ne hari na biyu da aka kai wani sansanin soji a jihar Borno, a cikin makonni biyu.
A ranar Litinin rundunar sojan Nijeriya ta ce ta kashe gomman 'yan Boko Harama a wasu jerin hare-hare da rundunar ta ƙaddamar a yankin Ladin Battu a dajin Smabisa ranar Lahadi.
Sanarwar, wadda muƙaddashin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin kai, keftin Reuben Kovangiya ya fitar ta ce Ladin Battu wani muhimmin wuri ne da ‘yan ta’adda ke amfani da shi wajen shirya hare-hare.
Boko Haram, wadda aka kafa tun farkon shekarun 2000, ta ƙaddamar da hare-haren ta’addanci tun shekarar 2009, lamarin da ya sanadin salwantar dubban mutane.
Comments
No comments Yet
Comment