Sport
Dollar
38,8033
0.05 %Euro
43,4598
0.92 %Gram Gold
4.052,5000
0.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tuntuɓar baya bayan nan a yaƙin Rasha da Ukraine sun kawo sabbin damarmaki, in ji shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yana mai ƙara wa da cewa ya yi amanna wannan dama ‘ba za ta lalace ba’.
Turkiyya ta zama ƙasar da duniya ke yi wa kallon babbar mai taka rawa a diflomasiyyar zaman lafiya, da tallafi ga duniya, da taimako, da shiga tsakani, kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana.
“Tun da fari, mun tattauna da shugaban Ukraine Vladimir Zelensky. A makon da ya gabata, mun tattauna hakan da shugaba Trump, mun tattauna kan hanyoyin da za a bi don dakatar da zubar da jini,” in ji Recep Tayyip Erdogan bayan jagorantar taron majalisar ministoci a Ankara a ranar Litinin.
“Muna goyon bayan aniyar abokina shugaban Amurka Donald Trump ta warware manyan rikice-rikice ta hanyar diflomasiyya. Godiya ga Allah, Turkiyya ta zama ƙasar da ake naman ta taimaka, ta tallafa da shiga tsakani a diflomasiyyar zaman lafiya ta duniya.”
Game da ƙoƙarin da ake ci gaba da yi na kawo ƙarshen rikicin Rasha da Ukraine, wanda a yanzu ya shiga shekararsa ta hudu, a cewar Erdogan “A matsayin ƙasar da dukkan ɓangarorin suka amince da ita,” Turkiyya ta shirya bayar da gudunmawa ga taron zaman lafiya na Rasha-Ukraine da za a yi a ranar Alhamis a Istanbul, kuma yana mai farin cikin karɓar baƙuncinsu.
Tuntuɓar baya bayan nan a yaƙin Rasha da Ukraine sun kawo sabbin damarmaki, in ji shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yana mai ƙarawa da cewa ya yi amanna wannan dama ‘ba za ta lalace ba’.
Game da tashin tashina tsakanin Pakistan da India, Erdogan ya yi maraba da sanar da tsagaita wuta da ɓangarorin suka yi, inda ya yi kira gare su da su guji tsokanar juna.
Game da sanarwar da ‘yan ta’addar PKK suka fitar ta rushe kanta da ajiye makamai, Erdogan ya ce wannan muhimmin mataki ne ga tsaron Turkiyya, da zaman lafiyar yanki da haɗin kan ƙasa mai ɗorewa.
“Muna kallon sanarwar rusa PKK a matsayin mataki da ya haɗa da dukkan rassanta, musamman a arewacin Iraƙi, da Syria da Turai.” in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment