Dollar

38,6128

0.11 %

Euro

43,8359

0.34 %

Gram Gold

4.200,1200

1.6 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Manufar Amurka ita ce a "hanzarta samun zaman lafiya da wadata da zai sa Turkiyya da Amurka su ƙara ci gaba da kuma inganta duniya," in ji Thomas Barrack.

Trump na son ƙawance tsakanin Amurka da Turkiyya ta ƙara ƙarfi, in ji sabon jakadan Amurka a Ankara

Munafar Shugaban Amurka Donald Trump ita ce ɗaukaka matakin ƙawancen Turkiyya da Amurka zuwa matakin da “ya dace da ita,” kamar yadda sabon jakadan Amurka a Turkiyya ya bayyana.

"Na zo da saƙo mai sauƙi daga Shugaba Trump…wanda shi ne shawarsa ta ɗaukaka matakin ƙawancen Turkiyya da Amurka zuwa matakin da ya dace da ita," kamar yadda Thomas Barrack ya shaida wa manema labarai ranar Litinin a filin jiragen saman Esenboga a babban birnin ƙasar Turkiyya Ankara.

Yayin da yake bayyana [jin] karamcin kasancewa a ƙasar kakanninsa, Barrack ya ƙara da cewa Washington da Ankara sun daɗe suna kasancewa masu "alaƙa mai kyau," yana mai jaddada buƙatar da ke akwai ta mayar da dangantakar "ta musamman."

"Manufar shugaban ƙasar ita ce ya ɗaukaka ta hanyar mutane da kuma ta hanyar manyan shuwaganin ƙasashen biyu, domin samun zaman lafiya da wadata cikin hanzari da zai sa Turkiyya da Amurka su ƙara ɗaukaka kuma duniya ta ƙara inganta," in ji shi.

A makon jiya ne majalisar dattawan Amurka ta tabbatar da Barrack a matsayin jakadan ƙasar zuwa Turkiyya a wata ƙuri’ar da aka ƙada zauren majalisar inda 60 suka goyi baya, kuma 36 suka ƙi.

Muhimmancin Turkiyya

Barrack, wanda ya daɗe yana abokantaka da Trump kuma wanda ya kasance sanannen ɗan kasuwa, zai kama aiki ne a wani lokacin da dangaka ke sauyawa tsakanin ƙasashen biyu.

A lokacin ba’asin tabbatar da naɗinsa a gaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar dattawan Amurka a watan da ya gabata, Barrack ya jaddada muhimmancin kasancewar Turkiyya ƙawar Amurka.

Barrack, mai shekara 78, an haife shi kuma ya tashi ne a kudancin California. Yana da shaidar karatun digiri daga jami’ar Southern California da kuma kwalejin sharia’a ta jami’ar San Diego.

Mutumin da aka sani da alaƙarsa ta ƙut-da-ƙut da Trump shi ya jagorancin kwamitin da ta shirya bikin rantsar da Trump a shekarar 2017 kuma ya kasance muhimmin mai ba da shawara a yaƙin neman zaɓenshi na shekarar 2016.

Barrack ya gaji ambasada Jeff Flake, wanda ya yi aiki daga watan Janairun shekarar 2022 zuwa watan Satumbar shekarar 2024. Muƙamin ya kasance ba kowa a kai tun bayan tafiyar Flake.

Erdogan da Trump sun yi tattaunawa ‘mai amfani sosai'

Daga farko ranar Litinin, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce wayar da ya yi da Trump ta kasance "mai amfani sosai, cikakkiya da kuma mai gaskiya."

"A yau, wayar da na yi da Shugaban Amurka, abokina Mista Donald Trump, ta kasance mai amfani sosai, ta kasance cikakkiy kuma mai gaskiya," kamar yadda Erdogan ya wallafa a shafinsa na X bayan wayar.

"Ina fatan ganawa da abokina Trump nan gaba kaɗan," in ji Erdogan, yana mai bayyana fatan cewa ganarwasu " za ta kawo sakamako mai kyau ga ƙasashenmu."

Erdogan ya ce sun jaddada son da su biyun ke yi na ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannonin tsaro da cinikayya.

Shugabannin biyu sun tattauna wasu batutuwa ciki har da dangantaka tsakanin Turkiyya da Amurka da batun yaƙin Gaza da ababen da ke faruwa yanki da ma duniya.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#