Dollar

38,7504

-0.11 %

Euro

43,4576

0 %

Gram Gold

3.964,7200

-2.19 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin Nijeriya, ciki har da kisan sojoji a garin Marte.

Boko Haram: Majalisar dattawan Nijeriya ta nemi a tura ƙarin sojoji Borno da Yobe

Majalisar dattawan Nijeriya ranar Talata ta buƙaci rundunar sojin ƙasar ta ƙara tura sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. 

Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram, fadar ƙaramar hukumar Nganzai, da sanyin safiyar ranar Talata.

A wani ƙudurin da mai tswatarwa majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar, ‘yan majalisar sun ce duk da cewa a baya kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomin jihar Borno sun kasance ƙarƙashin ƙarƙashin ikon ‘yan Boko Haram, haɗin kai tsakanin sojoji da ‘yan sakai ya taimaka wajen ƙwato ƙananan hukumomin.

Amman zaman lafiyan da aka samu, ya sa hedikwatar yaƙi da ta’addancin ta koma arewa maso yammacin ƙasar inda sojin ƙasar ke yaƙi da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Yayin da yake nuna damuwa game da yadda ‘yan ta’addan ke sauya dabarun yaƙin su, Monguno ya bayyana yadda ƙungiyar ke amfani da na’urorin zamani ciki har da jirage mara matuƙa da kuma ƙarin amfani da abubuwan fashewa da suka ƙera da kansu, lamarin da ya janyo mace-macen fararen hula da sojoji da kuma katse harkokin sufuri.

Bayan haka ne majalisar dattawan Nijeriyar ta yi kira ga shugabannin sojin ƙasar su tura isassun sojoji zuwa arewa maso gabashin ƙasar su kuma tabbatar da cewa an ba su na’urorin zamani domin su daƙile sabuwar barazanar.

Kazalika majalisar ta nemi kwamitinta kan sojin ƙasa da na sama ya sa ido tare da tabbatar da cewa sojojin sun bi umarnin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#