Sport
Dollar
38,8541
-0.09 %Euro
44,2289
0.23 %Gram Gold
4.175,2600
0.78 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Akwai ƙasashe 91 a duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) yake bin su bashi, inda Afirka take da ƙasashe 47, waɗanda su ne 52% na ƙasashen da ake bi bashin.
Asusun Lamuni na Duniya (IMF) yana bin ƙasashe arba’in da bakwai a Afirka bashin kuɗin da ya kama daga miliyoyi zuwa biliyoyin dalolin Amurka, inda Masar take kan gaba cikin waɗanda suka ci bashin, yayin da Lesotho take da mafi ƙarancin bashin.
Ƙasashen Afirka uku — Botswana da Eritrea da Libiya — ba su taɓa karɓar bashin IMF ba.
An cire Nijeriya daga cikin jerin, wacce ta biya bashin IMF na dala biliyan 3.4 a Afrilun 2025.
A lokuta da dama a baya bayan nan, IMF ta hana Zimbabwe bashin, inda ta ambato ɗimbin bashin da ake bin ƙasar, wanda ke barazanar cewa da wuya ta iya biya.
Ƙasashen Afirka ne suka karɓi 52% na bashin IMF
Mauritius na daga ƙasashen da su ma ba sa cikin waɗanda ake bi bashin.
Akwai ƙasashe 91 a duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) yake bin su bashi, inda Afirka take da ƙasashe 47, waɗanda suke su ne 52% na ƙasashen da ake bi bashin.
Ƙasar Argentina, wacce ake bi bashin dala biliyan 40.3 ita ce a kan gaba cikin jerin waɗanda IMF yake bi bashin, sai Ukraine da ake bi dala biliyan 10.8 da Masar da ake bi bashin dala biliyan 8.5.
IMF ita ce ƙarshen inda ake zuwa neman bashi, ma’ana yana bayar da bashin da zai warware wasu matsaloli ne ko kuma lokacin da aka shiga mawuyacin hali, amma ba ya bayar da bashi don ayyukan ci-gaba ko wasu abubuwa makamantan haka.
Ka’idojin karɓar bashin
Sai dai kafin IMF ya bayar da bashi, yana sanya ƙa’idoji ga ƙasashen da suke cin bashin.
Ƙa’idojin za su iya ƙunsar soke wasu hukumomin gwamnati, ko fito da sabbin haraje-haraje, ko dakatar da wasu shirye-shirye na bayar da tallafi kamar tallafin abinci da na ma fetur.
Ga jerin ƙasashen Afirka da IMF ke bi bashi, da abin da yake bin kowace ƙasa, zuwa 13 ga watan Mayun 2025, kamar yadda bayanan da IMF ta wallafa suka nuna.
1. Masar – $8.5b
2. Kenya – $3b
3. Angola – $2.8b
4. Côte d'Ivoire – $2.6b
5. Ghana – $2.4b
6. DRC – $1.8b
7. Ethiopia – $1.4b
8. Kamaru – $1.2b
9. Senegal – $1b
10. Tanzaniya – $1b
11. Zambiya – $993m
12. Uganda – $993m
13. Sudan – $992m
14. Maroko – $938m
15. Benin – $715m
16. Madagascar – $702m
17. Ruwanda – $607m
18. Tunisiya – $579m
19. Mozambique – $545m
20. Chadi – $468m
21. Gabon – $440m
22. Nijar – $420m
23. Mali – $418m
24. Afirka ta Kudu – $381m
25. Jamhuriyar Kongo – $353m
26. Saliyo – $337m
27. Guinea – $327m
28. Burkina Faso – $324m
29. Malawi – $308m
30. Mauritania – $305m
31. Togo – $303m
32. Sudan ta Kudu – $246m
33. Jamhuriyar Tsakiyar Afirka – $200m
34. Laberiya – $181m
35. Gambiya – $117m
36. Burundi – $100m
37. Seychelles – $97m
38. Namibiya – $96m
39. Somaliya – $87m
40. Cape Verde – $72m
41. Equatorial Guinea – $60m
42. Guinea-Bissau – $52m
43. Djibouti – $32m
44. Sao Tome and Principe – $27m
45. Comoros – $19.9m
46. Eswatini – $19.6m
47. Lesotho – $11.7m
48. Botswana (ba taɓa karɓar bashin IMF ba)
49. Libya (ba taɓa karɓar bashin IMF ba)
50. Eritrea (ba taɓa karɓar bashin IMF ba)
51. Nijeriya (ta biya bashin IMF na $3.4b a Afrilun 2025)
52. Aljeria (ta ƙi karɓar bashin a 2020)
53. Zimbabwe (IMF ya ƙi amincewa ya ƙara maba bashi a 2021)
54. Mauritius (ba ta cikin jerin)
Comments
No comments Yet
Comment