Sport
Dollar
38,8859
0.04 %Euro
44,0969
0.01 %Gram Gold
4.134,0400
-0.21 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%“Ba zan iya cewa ɗari bisa ɗari duk waɗanda suka miƙa wuya suna abin da ya dace ba, amma ina son in tabbatar muku cewa sama da kashi 99 cikin 100 suna abin da ya dace kuma ba su da hannu a cikin ta’addanci,” in ji Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasar Nijeriya da ma wasu sojojin ƙasar suna taimaka wa ‘yan Boko Haram wajen kwarmata musu bayanan sirrin ƙasar.
Zulum ya yi wannan zargin ne ranar Laraba a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin ɗin News Central inda ya lashi takobin cewa gwamnatin jiharsa za ta ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri a jihar tare da hukunta masu yi wa harkar tsaro zagon ƙasa.
“Akwai masu kwarmata bayanai da kuma masu haɗa baki [da Boko Haram] cikin sojojin Nijeriya da ‘yan siyasa da ma masu zama cikin jama’a. Abin da za mu yi shi ne mu ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirrinmu kuma mu hukunta su babu ƙaƙƙautawa,” in ji gwamnan .
“Idan muka kawar da harkar kwangila, cikin watanni shida kawai za mu kawo ƙarshen wannan haukar. Ba ma buƙatar mu siyasantar da rashin tsaro,” in ji gwamnan.
‘Yan ta’addan da suka miƙa wuya
A lokacin da yake bayani game da lamarin masu tayar da ƙayar bayan da suka miƙa wuya, Zulum ya ce duk da cewa ba dukkan ‘yan ta’addan da suka miƙa wuya ne suka gayra halayansu gabaɗaya ba, yawancinsu suna ba da gudumawa mai kyau cikin al’umma.
“Ba za ni iya cewa ɗari bisa ɗari duk waɗanda suka miƙa wuya suna abin da ya dace ba, amma ina son in tabbar muku cewa sama da kashi 99 cikin 100 suna abin da ya dace kuma ba su da hannu a cikin ta’addanci,” in ji Zulum
Gwamnan ya sake tabbatar da buƙatar da ke akwai wa Nijeriya ta rungumi dabarun ƙarfi da dabarun da ba na ƙarfi ba wajen tunkarar tayar da ƙayar baya, yana mai cewa sama da kashi 99 cikin 100 na ‘yan ta’addan da suka tuba ba su da hannu a ta’addanci.
Ya jaddada cewa ƙarfin soji kawai ba zai iya kawo ƙarshen ta’addancin gaba ɗaya ba.
Ya bayyana cewa, “ƙarfin soji kawai ba zai iya kawo ƙarshen ta’addanci ba. Dole mu tabbatar cewa an yi amfani da dabarun da ba na soji ba yadda ya kamata.”
“Abin da nake nufi da dabarun da ba na soji ba shi ne ɓullo wa matsalar ta hanyoyin zamantakewa da da siyasa da kuma tattalin arziƙi.
“Dabarun da ba na ƙarfi ba da muke amfani da su a halin yanzu suna ba da sakamako mai kyau tare da tallafin sojin Nijeriya.”
Comments
No comments Yet
Comment