Dollar

38,9163

0.11 %

Euro

44,1784

0.17 %

Gram Gold

4.114,7500

-0.68 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A cikin watan Afrilun shekarar 2025 ne dai wata kotun birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja ta kori ƙarar da Emefiele ya shigar ta neman a soke ƙwace gidajen domin ba a ba shi damar kare kansa game da mallakar gidajen.

EFCC ta mika gidaje 753 da aka ƙwace daga Emefiele ga Ma’aikatar Gidaje ta Nijeriya

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Nijeriya zagon ƙasa (EFCC) ta miƙa gidaje da ta ƙwace daga tsohon gwmanan bankin ƙasar, Godwin Emefiele, ga Ma’aikatar Gidajen ƙasar.

Wata sanarwar da hukumar ta EFCC ta fitar ta ce shugaban hukumar Mista Ola Olukoyede, ne ya miƙa gidajen ga Ministan Gidaje Ahmed Dangiwa a hedikwatar ma’aikatar da ke unguwar Mabushi a Abuja ranar Talata.

Sanarwar ta ambato shugaban na EFCC yana cewa miƙa gidajen zai “nuna wa ‘yan Nijeriya cewa dukkan kadarar haram da muka ƙwato a cikin aikinmu za a bayyana yadda aka yi da shi ga ‘yan Nijeriya domin kada a bari a sake satar kuɗin sata.”

“Yana da muhimmanci mu jaddada wa ‘yan Nijeriya cewa yaƙi da cin hanci da rashawa zai iya aiki kuma za mu iya sa shi ya yi aiki, kuma ɗaya daga cikin muhimman dalilan da za su sa yaƙi da cin hanci ya yi tasiri shi ne mu hana waɗanda suka saci arzikinmu jin daɗin sa,” in ji shugaban na EFCC.

A cikin watan Afrilun shekarar 2025 ne dai wata kotun birnin Tarayyar Nijeriya Abuja da ke unguwar Apo ta kori ƙarar da Emefiele ya shigar ta neman a soke ƙwace gidajen domin ba a ba shi damar kare kansa game da mallakar gidajen ba.

Godwin Emefiele ne tsohon babban gwamnan babban bankin Nijeriya kafin Gwamnan Babban Bankin ƙasar mai ci ya karɓi ragamar bankin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#