Sport
Dollar
38,8512
0.29 %Euro
43,5442
-0.02 %Gram Gold
4.048,7400
0.38 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilu.
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da sabbin bayanan ƙididdiga inda ta bayyana cewa an samu raguwar tashin farashin kayayyaki a ƙasar.
A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilun 2025.
A bara ne dai aka samu hauhawar farashin da aka shafe gomman shekaru ba a samu irinsa ba a ƙasar biyo bayan matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na karya darajar naira da kuma cire tallafin man fetur a lokacin da ya hau mulki a 2023.
Haka kuma a binciken da NBS ɗin ta yi a matakin shekara, an samu raguwa a hauhawar farashi daga kaso 38.80 cikin 100 a watan Disamba zuwa 24.48 a watan Janairu.
An ƙara samun raguwa a watan Fabrairu kafin ya ƙaru a Maris.
Wani rahoto da NBS ɗin ta fitar ya nuna cewa a kayayyakin abinci da kuma barasa ne aka fi samun hawa da saukar farashi.
A watan Maris, hauhawar farashin kayan abinci na kan 21.79 inda a watan Afrilu ya sauka zuwa 21.26.
Comments
No comments Yet
Comment