Sport
Dollar
38,7037
-0.19 %Euro
43,4929
0.16 %Gram Gold
4.012,2000
1.29 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin magance matsalolin yawan ɗauke wuta a faɗin ƙasar.
Ministan lantarkin Nijeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Nijeriya na buƙatar zuba jarin dala biliyan 10 a kowace shekara na tsawon shekaru 20 kafin ƙasar ta samu lantarki mai ɗorewa.
Da yake magana a wajen ƙaddamar da wani aikin samar da lantarki ta hanyoyi biyu (hanyar da aka saba samar da lantarki da hanyar hasken rana) mai ƙarfin megawat 2.5 a makarantar horas da sojojin Nijeriya da ke Kaduna (NDA), ministan ya bayyana rashin kula da rashin isasshen jari da kuma kasa inganta hanyoyin raba lantarki a matsayin muhimman matsalolin da suka samar da giɓin da ke da akwai a fannin lantarkin ƙasar.
Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin magance matsalolin rashin wuta a faɗin ƙasar.
Ministan ya bayyana jajircewar gwamnatin wajen samar da makamashi mai ɗorewa da za a iya dogaro a kai ga muhimman cibiyoyin gwamnati kamar NDA.
“Domin mu samu lantarki mai ɗorewa da za a iya dogaro a kai, muna buƙatar aƙalla dala biliyan 10 a kowace shekara nan da shekara 20 masu zuwa. Amma akwai wasu muhimman matsalolin da ya kamata a magance idan ana son kashe waɗannan kuɗaɗen ya ba da ma’ana,” in ji shi.
Adelabu ya ce rattaɓa hannu kan dokar makamashi ɗaya ne daga cikin muhimman matakan da gwamnati ta ɗauka wajen magance matsalolin fannin lantarkin ƙasar.
“Wannan dokar ta yi nasarar ‘yanta fannin lantarkin tare da bai wa kowane mataki na gwamnati ‘yancin taka rawa domin samar wa ‘yan ƙasa lantarki.
Comments
No comments Yet
Comment