Dollar

38,8013

0.07 %

Euro

43,1016

-1.33 %

Gram Gold

4.033,8900

-2.65 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A ranar Asabar, Putin ya yi kira ga shugabannin Kiev da su dawo tattaunawa a Istanbul a ranar Alhamis 15 ga Mayu.

Zelensky ya amince da shawarar shugaban Rasha ta dawo da tattaunawar zaman lafiya a Istanbul

Shugaban Ukraine Vladimir Zelensky ya ce da kansa zai jira Shugaban Rasha a Turkiyya a ranar Alhamis, a yayin da kokarin diflomasiyya ke bayyana dawo da tattaunawar da aka dakatar watannin baya tsakanin ƙasashen biyu.

Muna sauraron tsagaita wuta mai dorewa, daga gobe, don samar da tushen assasa diflomasiyya,” in ji Zelensky ta shafinsa na X a ranar Lahadi.

“Babu buƙatar tsawaita kashe mutane, Kuma zan jira Putin a Turkiyya a ranar Alhamis. Ni da kaina. Ina fata wannan lokaci ne da Rashawa ba za su bayar da wani uzuri ba.”

Bayanin nasa ya zo ne jim kaɗan bayan Putin ya sanar da cewa Rasha ta shirya dawo wa tattaunawar kai tsaye da Ukraine a Istanbul daga ranar 15 ga Mayu.

A wani saƙo da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar ta shafin X, ya yi kira ga Ukraine da ta amince da shawarar ta Rasha.

“Shugaban Rasha ba ya san ƙulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta da Ukraine, amma dai yana son ganawa a ranar Alhamis, a Turkiyya, don tattauna yiwuwar kawo ƙarshen ZUBAR DA JINI. Ya kamata Ukraine ta amince da wannan NAN DA NAN… Na fara tantamar cewa Ukraine za ta ƙulla yarjejeniya da Putin wanda yana nan yana ta murnar Nasarar Yakin Duniya na II… KU GANA YANZU!!!”

Turkiyya ta yi maraba da shawarar Putin

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai a Moscow, Putin ya ce a ranar Litinin zai tattauna ta wayar tarho da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan don nema a hukumance ga Turkiyya ta karɓi baƙuncin tattaunawar.

“Rasha ta shirya tattaunawa ba tare da saka wasu sharuɗɗa ba,” in ji Putin.

Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da kalaman na Putin na a dawo tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul, yana mai cewa ya ji daɗin jin sa yana fadin cewa yana goyon bayan a ci gaba da tattaunawa daga inda aka tsaya a 2022.

Erdogan ya sake jaddada cewa Turkiyya a shirye take ta karɓi baƙuncin tattaunawar da ke da manufar samun mafita ta ƙarshe.

Turkiyya ta karɓi bakuncin tattaunawa da dama a 2022 - bayan fara rikicin - da manufar kawo ƙarshen rikicin.

Shugaba Erdogan da ya sha samun nasarar warware rikice-rikice, yana yawan bayyana cewar Turkiyya a shirye take don karɓar baƙuncin tattaunawar zaman lafiya ta kuma yi duk mai yiwuwa wajen warware rikicin.

Turkiyya na da kyakkyawar alaka da kasashen Rasha da Ukraine.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#