Sport
Dollar
38,8024
-0.02 %Euro
43,4485
-0.19 %Gram Gold
3.964,8400
-2.19 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Trump ya ce Yarima Mai Jiran Gado na Sudiyya Mohammed bin Salman da Shugaban Turkiyy Recep Tayyip Erdogan ne suka ƙarfafa masa gwiwa kan ya gana da Alsharaa.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da Shugaban Amurka Donald Trump, da Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman da Shugaban Syria Ahmed Alsharaa sun yi wata ganawa ta yanar gizo, in ji kamfanin dillancin labarai na Anadolu a safiyar Laraba.
Shugaban Turkiyya ya ce matakin shugaban Amurka na janye takunkuman da aka saka wa Syria na da muhimmanci a tarihi.
A Riyadh, a ziyarar aiki ta farko da ya kai ƙasar wajen tun bayan dawo wa mulki a karo na biyu, ya zama shugaban kasar Amurka na farko da ya gana da shugaban kasar Syria.
Shugabannin biyu sun yi ganawa kafin babban taron shugabannin kasashen Yankin Tekun Fasha a Saudiyya a yayin ziyarar Trump a yankin, kamar yadda wani jami’in Fadar White House ya bayyana.
Babu wani shugaban Amurka da ya gana da shugaban Siriya tun bayan Bill Clinton da ya gana da Hafez Al Assad, mahaifin Bashar Al Assad a Geneva a shekarar 2000.
A ranar Talata Trump ya sanar da cewa zai janye “munanan” takunkuman da aka saka wa Siriya a zamanin Assad waɗanda ke karya tattalin arziki.
Matakin amsa ne ga kiran da ƙawayen Alsharaa Turkiyya da Saudiyya suka yi.
Isra’ila ta nuna rashin amincewar ta ga janye takunkuman, amma a ranar Talata Trump ya ce bin Salman da Erdogan ne suka ƙarfafa masa gwiwar janye takunkuman.
Trump ya ce ‘lokacin shanawar Syria’ ne yanzu kuma sauƙaƙa mata takunkuman zai ba su damar haɓaka.
‘Yan Siriya sun yi murnar samun wannan labarin, inda maza, mata da yara da yawa suka taru a dandalin Umayyad na Damascus.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Siriya ta bayyana matakin na Trump da “Gaba mai muhimmanci” da zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali da lumana
Ziyarar Trump a Gabas ta Tsakiya
Rana ta farko ta ziyarar Trump a Gabas ta Tsakiya ta samu muhimman bukukuwa inda Saudiyya ta sha alwashin zuba jarin dala biliyan 600 a Amurka a kuma sayen makamai na dala biliyan 142 daga Amurkan.
Daga baya a ranar Laraba Trump ya wuce zuwa babban birnin Qatar Doha, domin ganawa da Sarki Tamim bin Hamd AlThani da sauran jami’an gwamnati.
Qatar, babbar ƙawar Amurka, ana sa ran za ta sanar da zuba jarin biliyoyin daloli a Amurka.
Bayan ziyartar Qatar, Trump zai wuce Abu Dhabi, inda zai gana da shugabannin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Alhamis.
Daga nan ne zai koma gida Washington a ranar Juma’a, amma ya ce akwai yiwuwar ya bi ta Turkiyya don halartar ganawar da Shugaban Rasha Vladimir Putin zai yi da Shugaban Ukraine Vladimri Zelensky a Istanbul.
Comments
No comments Yet
Comment